Kyari: Kamfanin NNPC zai ba ‘Yan Najeriya 50, 000 abin yi (Bidiyo)

Kyari: Kamfanin NNPC zai ba ‘Yan Najeriya 50, 000 abin yi (Bidiyo)

A wani bidiyo da ya shigo hannumu a Ranar 13 ga Watan Disamban 2019, mun ji cewa kamfanin man Najeriya watau NNPC, zai ba mutum 50, 000 da su ka kammala makaranta, abin yi.

Kamfanin ya yi wannan alwashi ne ta bakin babban shugabansa a karshen makon nan. MD Mele Kolo Kyari ya yi wannan albishiri ne wajen wani taro da kamfanin NLNG na mai da gas ya shirya

Mele Kolo Kyari ya ke cewa kamfanin NNPC na neman yadda zai samawa mutum 10, 000 aiki kai-tsaye, sai kuma wasu 40, 000 da za su amfana daga gefe domin a taimaki matasa aikin yi.

Malam Mele Kyari ya kara shaidawa Duniya a wannan faifen bidiyo cewa NNPC zai samawa Najeriya Dala biliyan 9 na kudin shiga, sannan ya bunkasa harkar kasuwanci a fadin kasar nan.

Mu na shirin samawa mutum 10, 000 aiki kai-tsaye a kasar nan, da kuma wasu mutane 40, 000 da za su amfana daga wadannan ayyuka a gefe, sannan kuma da Dala biliyan $9 ga asusun kasa.”

Shugaban na NNPC ya cigaba da cewa: “Za mu inganta saha’anin kasuwanci a kaf fadin kasar nan” Mele Kyari ya bayyana cewa NNPC zai yi wannan aiki ne ba tare da bata wani lokaci ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel