Mai girma Sultan ya yi gargadi a game da yi wa kotu rashin da’a

Mai girma Sultan ya yi gargadi a game da yi wa kotu rashin da’a

A Ranar Alhamis, 12 ga Watan Disamban 2019, Mai girma Sarkin Musulmi watau Sultan na kasar Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar II, ya yi gargadi game da rashin bin hukuncin Alkalan kotu.

Sarkin Musulmin ya nuna cewa sabawa umarnin kotu zai jawo rashin aiki da doka a kasar nan. Sa’ad Abubakar II ya yi wannan jawabi ne da ya ke magana a wajen wani taro a Garin Abuja.

Hukumar NIREC ta addinan Najeriya ce ta gudanar da taron zangon karshe na wannan shekarar wanda ta yi a kan tasirin Malamai da kungiyoyi wajen kawo zaman lafiya da cigaban kasa.

Daily Trust ta ce Sultan ya ja kunne da a rika bin dokar da aka gindaya. Sai dai bai kama sunan kowa a wajen wannan jawabi ba, amma ya nuna goyon baya ga tsarin shugabancin kama-kama.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Amurka ya nemi Gwamnatin Najeriya ta rika bin doka

Mai girma Sultan ya yi gargadi a game da yi kotu rashin da’a

Sultan Sa’ad Abubakar II ya ce rashin bin doka ya na da hadari
Source: Depositphotos

Jaridar ta rahoto cewa Mai girma Sultan ya yi kira da kowa ya zama mai bin doka a Najeriya. Ya ce: “Dole mu rika bon dokar kasar mu a koyaushe. Bai kamata mu rika watsi da dokokinmu ba.”

“Idan kotu ta yanke hukunci, to ayi maza a zartar ba tare da bata lokaci ba. Babu al’ummar da za ta iya cigaba ba tare da ta rika bin dokoki ba. Komai matsayinka, dole ka bi doka.” Inji Mai girma.

Sultan ya nuna cewa rashin bin umarnin da kotu ta yi ya na da illa. Ya ke cewa: “Idan ba ka gamsu da shari’a ba, sai ka daukaka kara, amma ba ka tubure ka yi watsi da hukuncin Alkali ba.”

“Idan ka yi watsi da umarnin kotu saboda ka na gwama ko shugaban kasa ko wani babba a kasa, ka kafa mummunan tarihi ne da za ayi koyi da shi. Dole ‘yan kasa su zama masu aiki da doka.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel