Sanarwa: Daga watan Disambar nan manhajar WhatsApp za ta daina aiki a wayoyin mutane da dama

Sanarwa: Daga watan Disambar nan manhajar WhatsApp za ta daina aiki a wayoyin mutane da dama

- Kamfanin kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp ya bayyana cewa, manhajarsu zata dena aiki a wasu wayoyin

- Kamfanin ya ce, bashi da tsarin da zai ba manhajar damar aiki a wasu tsoffin wayoyi

- Wannan sabon tsarin zai fara aiki ne a ranar 31 ga watan Disamba

Kafar sada zumunta ta WhatsApp ta sanar da cewa nan ba da dadewa ba zata dena aiki a miliyoyin wayoyi a fadin duniya.

Akwai yuwuwar masu amfani da kafar a tsoffin wayoyi masu yawa zasu kasa amfani dashi.

Kafar ta bayyana hakan ne ta shafin Facebook cewa zata dena aiki a wadansu wayoyi a ranar 31 ga watan Disamba 2019.

Kamfanin ya ce duk wata waya da ke aiki da tsarin Windows Mobile zata daina amincewa da ita.

Amma kuma, ba su kenan ba. Duk wata waya kirar IPhone mai tsohon IOS ba zata iya amfani da kafar ba. Hakazalika duk wata waya mai karfin 2.3.7 ba zata iya amfani da kafar ba.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya mayar da naira miliyan 98 da aka yi kuskuren turawa asusun bankin shi

Tsarin IOS din da na Android din ba zasu fara aiki ba har sai 1 ga watan Fabrairu, 2020. Kamfanin ya ce, duk mai amfani da irin tsoffin wayoyin nan ba zasu iya amfani ko bude sabon asusu na kafar sada zumuntar.

"Saboda rashin shirinmu da wadannan cigaban, akwai yuwuwar su dena aiki a kowanne lokaci," kamfanin ya bayyana hakan ne a wata wallafa tashi.

Dama can dai, kafar sada zumuntar kan dena aiki a wasu lokutan, amma suna dawo aiki matukar mutum ya kara sauke wata manhajar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel