Dan Najeriya ya mayar da naira miliyan 98 da aka yi kuskuren turawa asusun bankin shi

Dan Najeriya ya mayar da naira miliyan 98 da aka yi kuskuren turawa asusun bankin shi

- Wani dan Najeriya mai suna Sunny Anderson ya bayyana yadda ya mayar da wasu makuden kudi da aka tura a asusun bankinshi bisa ga kuskure

- Anderson ya bayyana yadda wani kamfani da ke zama a Abuja ya yi kuskuren tura mishi naira miliyan 98

- Ya yi fatan Ubangiji ya kare shi daga cin abinda ba nashi ba, komai tsananin talaucin da ya addabeshi

Wani dan Najeriya mai suna Sunny Anderson ya bayyana yadda ya mayar da naira miliyan 98 da aka saka a asusun bankinshi a bisa kuskure. Anderson ya wallafa hakan ne a shafinsa na wata kafar sada zumuntar zamani.

Ya bayyana labarinshi tare da addu'ar afuwa ga 'yan Najeriya. Yayi fatan 'yan Najeriya zasu iya mayar da duk abinda ba nasu ba zuwa mamallakan abun.

Ya wallafa kamar haka: "A yau, Ubangiji ya bani damar mayar da makuden kudade har naira miliyan 98 da aka tura asusun bankina cikin kuskure. Wani kamfani ne da ka zama a Abuja ya yi kuskuren. Ubangiji ba zai bamu damar daukar abinda ba namu ma, komai tsananin talaunci".

KU KARANTA: Kotu ta yankewa Umaru hukuncin kisa a jihar Bauchi, bayan an kama shi da laifin kashe mahaifinsa

Wannan dai ba shine karo na farko da aka fara samun mutane irinshi masu tsoron Allah ba, a lokuta da dama akan samu wasu su mayar da abubuwan da ba na su ba, irinsu kudade, wayoyi da sauransu.

A karshe mutumin yayi kira ga 'yan Najeriya talakawa da shugabanni da su dinga jin tsoron Allah suna mayar da duk wani abu da ba nasu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel