Kotu ta yankewa Umaru hukuncin kisa a jihar Bauchi, bayan an kama shi da laifin kashe mahaifinsa

Kotu ta yankewa Umaru hukuncin kisa a jihar Bauchi, bayan an kama shi da laifin kashe mahaifinsa

- Wata babbar kotun jihar Bauchi ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Bayan gamsassun hujjoji da alkalin ya samu, an gano cewa Jauro ya bi mahaifinshi har cikin masallaci kuma ya daddatsa shi

- Duk da cewa Jauro ya musanta aikata laifin, shaidu goma kwarara sun tabbatar da aukuwar lamarin

Wata babbar kotun jihar Bauchi ta yanke wa wani mutum mai suna Umaru Jauro-Ori, hukuncin kisa. Jauro ya samu hukuncin nan ne bayan da aka kama shi da laifin kisan mahaifinsa a cikin masallaci a kauyen Mai'aduwa, karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Jastis Aliyu Usman ya kama Jauro da laifin kisan kai bayan shaidu gamsassu da ya samu.

A hukuncinsa, Usman ya ce, "mutuwar ta biyo bayan hannun wanda ake zargi da masu gurfanarwa suka tabbatar ta hanyar shaidu. Kotu ta gamsu, babu shakka cewa wanda ake karar ya aikata kisan kai. Wannan laifin yana da hukuncin kisa ne karkashin sashi na 221 na dokokin Penal Code. A don haka, na yanke mishi hukuncin kisa."

Kamar yadda shaidu suka bayyana, wanda ake zargin ya shiga masallaci a Mai'aduwa dauke da adda ya daddatsa mahaifinshi.

KU KARANTA: Wuce gona da iri: Jama'a ya kamata mu fara tausayawa Rahama Sadau - Datti Assalafiy

A sakamakon hakan ne mahaifin nashi ya samu munanan raunika. Bayan an hanzarta mika shi babban asibitin Misau, ya ce ga garinku saboda miyagun raunikan da ya ji.

Mai shari'ar ya tabbatar da cewa, Jauro ya musanta faruwar lamarin amma masu karar sun kawo shaidu gamsassu har 10. A shaidarsu daban-daban da kuma binciken 'yan sanda, alkali ya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya hallaka mahaifinshi.

Ya kara da bayyana cewa, dan uwan mamacin da kanin wanda ake zargin sun tabbatar wa da kotu cewa shi ya kashe mahaifinshi. Bayan kisan kuma, sai ya raba gadon mahaifinasu kuma ya bar kauyen na sama da watanni goma sannan ya dawo.

Matasan yankin ne suka cafke wanda ake zargin kuma suka mika shi ga hukumar 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel