Boko Haram sun kwace motocin Sojoji makare da makamai, sun kashe mutum 14

Boko Haram sun kwace motocin Sojoji makare da makamai, sun kashe mutum 14

Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kashe mutane 14 tare da jami’in rundunar Yansandan Najeriya guda daya a wani samame da suka kai jahar Borno dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru na AFP.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin matasa yan sa kai ne suka tabbatar da lamarin, inda suka ce yan ta’addan ISWAP ne suka kai harin a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba a cikin motocin yaki fiye da guda 12 a kauyen Mamuri dake jahar Borno.

KU KARANTA: Daga shekarar 2023 za mu daina shigo da man fetir daga kasashen waje – Shugaban NNPC

Wani matashin sa kai, Babakura Kolo yace: “Sun kashe mana mutane 14 da wani jami’in dansanda, da misalin karfe 8 na dare suka kaddamar da hari a kanmu a cikin motocin yaki guda 14, inda muka kwashe awanni muna fafatawa. Daga karshe makamanmu suka kare, don haka Boko Haram ci galaba a kanmu.”

A cikin wani sanarwa da Boko Haram ta fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da kai harin, inda tace mayakanta sun kashe Sojojin sa kai daga bangaren Najeriya guda 15, tare da kwatar motocin yaki guda biyu da suke dauke da tarin makamai da alburusai.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma gwamnatin kasar Nijar, tare da bayyana alhininsa bisa kisan da wasu gungun yan ta’adda suka yi ma dakarun Sojojin kasar Nijar guda 63 a garin Inates dake iyaka da kasar Mali.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, inda yace yan ta’addan sun fito ne daga kasar Mali, suka Nijar inda suka kashe Sojoji 63, ba’a san inda 34 suka shiga ba.

Buhari ya jaddada manufarsa na ganin ya kawo karshen ayyukan yan ta’adda a Najeriya da ma nahiyar Afirka gaba daya ta hanyar aikin hadin gwiwa da sauran kasashe dake makwabtaka da Najeriya, da kuma manyan kasashen duniya da kungiyoyi masu zaman kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel