Wajibi ne a hana 'Kafada Kemist' muddin ana son magance matsalar kwaya a Arewa

Wajibi ne a hana 'Kafada Kemist' muddin ana son magance matsalar kwaya a Arewa

Kungiyar fafutukan dakile ta'amuni da muggan kwayoyi a Arewa wato Drug Free Arewa Movement, DFAM ta yi kira ga gwamnati ta haramta sana'ar 'Kafada Kemist' a Arewacin NAjeriya domin magance kwaya.

Wata mambar kungiyar, Gambo Wakili, ya bayyana hakan ne yayinda take karanta jawabin da kungiyar ta saki bayan taron yaki da ta'amuni da kwaya cikin matasa da ya gudana a Abuja.

Gambo ta ce ya zama wajibi a kawar da wadannan masu sayar da maganin saboda su ke sayarwa matasa magungunan da suke cutarsu.

Ta yi kira gwamnonin jihohin Arewa 19, sarakunan gargajiya, yan majalisu da masu ruwa da tsaki su sanya hannu wajen yakin magance kwaya da sace-sacen yara.

A cewarta, lissafin da hukumar lissafi ta kasa wato NBS ta fitar kan ta'amuni da kwayoyi ya nuna cewa abin ya yi muni a Arewacin Najeriya

KU DUBA Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Najeriya daga Masar

Wajibi ne a hana 'Kafada Kemist' muddin ana son magance matsalar kwaya a Arewa

Wajibi ne a hana 'Kafada Kemist' muddin ana son magance matsalar kwaya a Arewa
Source: Facebook

A wani labarin daban, Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire ya koka kan hauhawan yan Najeriya dake sha tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, don haka yayi kira ga shuwagabannin makarantu da iyaye su zage damtse wajen magance matsalar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Osagie ya bayyana haka ne a yayin taron kasa a kan yaki amfani miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, inda ministan yace akwai yan Najeriya miliyan 14.3 da shekarunsu yake tsakanin 15 zuwa 64 dake shan miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel