Allah bashi da ɗa: Wata mata ta fizge amsa kuwwa daga hannun fasto yayin wa'azi a kasuwa

Allah bashi da ɗa: Wata mata ta fizge amsa kuwwa daga hannun fasto yayin wa'azi a kasuwa

Wata fusatacciyar mata musulma ta fuskanci wani faston Najeriya, ta kwace amsa kuwwa daga hannunshi. Matar wacce ta fusata da faston, ta yi yunkurin tarwatsa amsa kuwwa da ke tare da faston.

Dalilin yin hakan kuwa bai wuce cewa da faston ya yi ba “Yesu dan Ubangiji ne”.

Wannan lamarin ya faru ne a kasuwar Asaba da ke jihar Delta.

Kamar yadda kalaman bakin matar da ke ta kwarara ihu da kuka ke fita, “Allah bashi da ‘da”!!!

Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce daga ma’abota kafafen sada zumuntar zamani. Wasu daga cikin ma’abota amfani da kafar sada zumuntar sun jaddada cewa Allah bashi da ‘da, inda wasu suka ga wautarta da zakewarta a lamarin

DUBA WANNAN: Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

Amma Legit.ng ta ruwaito cewa, a shekarar 1977 ne Gary Miller, farfesan Lissafi a jami'ar Toronto da ke kasar Canada, ya dauki aniyar karanta Qur'ani domin gano kura - kuran dake cikinsa don nuna wa Musulman duniya cewa ba a kan hanyar gaskiya suke ba.

Farfesa Miller, mai tsaurin akidar addinin Kirista, ya dauki wannan niyya ne bayan ya lura cewa yana wahala Musulmi ya canja addini zuwa Kirista.

Abu na farko da farfesa Miller ya ce ya ci karo da shi a cikin Qur'ani, ba sau daya ba, shine kalubantar jama'a da aka a kan su yi amfani da hujja. "Shin ba zasu kasance masu kokonto a kan Qur'ani ba? da a ce wani ya saukar da Qur'ani ba Allah ba, to tabbas za a samu rudar wa a tattare da shi." (Qur'an 4:82).

"...idan kuma kun kasance masu a cikin masu kokonto a kan sakon da muko aiko shi Annabi Muhammad), ku gwada samar da wata Surah kamar wannan, sannan sai ku kwatanta." (Quran 2:23).

Bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana nazarin Qur'ani, farfesa Miller ya gamsu cewa maganganun dake cikin Qur'an su fi karfin a ce aikin mutum ne, a saboda haka ya karbi addinin Islama tare d cigaba da yin kira ga jama'a a kan su dawo hanyar gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel