Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Najeriya daga Masar

Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Najeriya daga Masar

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja bayan kwashe kwanaki biyu a birni Aswan, kasar Masar.

Shugaban kasan ya halarci taron zaman lafiya da cigaban nahiyar Afrika daya gudana ranar Laraba da Alhamis na watan Disamba, 2019.

Gabanin dawowarsa, shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Masar, AbdelFatah Sisi kan yadda za'a kawar da ta'addanci a nahiyar Afrika.

A taron Shugaba Muhammadu Buhari ya siffanta yin sulhu tsakanin kasashen hamayya a nahiyar Afrika shine babban hanyar kawo cigaba nahiyar gaba daya.

A matsayinmu da yan Afrika, yana da muhimmanci mu mayar da hankali kan dakile rikici da sulhu."

"Rikice-rikice na da hadari matuka ga al'ummarmu kuma yana kawo cikas wajen cigabanmu. Saboda haka, ba zamu gushe muna da'awar daina rikici ba." Yace

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Sauran ragowar 'yan tawagar shugaba Buhari sun hada da; Ministan tsaro, Bashir Magashi, karamin ministan harkokin kasashen ketare, Zubairu Dada, mai bawa shugaba kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da kuma babban darektan hukumar leken aisri ta kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel