Yan Najeriya miliyan 14 ne suke ta’ammali da miyagun kwayoyi – Ministan Buhari

Yan Najeriya miliyan 14 ne suke ta’ammali da miyagun kwayoyi – Ministan Buhari

Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire ya koka kan hauhawan yan Najeriya dake sha tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, don haka yayi kira ga shuwagabannin makarantu da iyaye su zage damtse wajen magance matsalar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Osagie ya bayyana haka ne a yayin taron kasa a kan yaki amfani miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, inda ministan yace akwai yan Najeriya miliyan 14.3 da shekarunsu yake tsakanin 15 zuwa 64 dake shan miyagun kwayoyi.

KU KARANTA: Kalaman Aisha Buhari sun tabbatar da Buhari cikakken dan siyasa ne – Yahaya Bello

Ministan yace wadannan rukunin yan Najeriya suna amfani da akalla daya daga cikin wadannan kayan shaye shaye; tabar wiwi, hodar iblis, kwayoyi da kuma miyagun allurai akalla sau daya a shekara daya.

Ministan wanda ya samu wakilcin shugaba kuma babban likitan asibitin kula da masu tabin hankali dake jahar Kaduna, Farfesa Abdulkareem Yusuf, ya bayyana cewa cututtukan dake da nasaba da miyagun kwayoyi suna karuwa a duniya.

“Iyaye, musamman iyaye mata da malamai suna da rawar da zasu taka wajen yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi, ya kamata su samar da isashshen lokaci da zasu tarbiyantar da yaran dake karkashin ikonsu domin su zamato matasan daya kamata abin alfahari a cikin al’umma.

“Duk da cewa rayuwa ya yi wahala a yanzu, akwai karayar tattalin arziki da talauci, amma hakan bai zama uzuri bag a sauke nauyin daya rataya a wuyanmu a matsayin na iyaye da malamai.” Inji shi.

A wani labarin kuma, babban Alkalin Alkalan Najeriya, mai sharia Ibrahim Tanko Muhammad ya nemi a gudanar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai kunshi tanade tanaden shari’ar Musulunci a cikinsa.

Alkali Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron Alkalan Najeriya karo na 20 dake gudana a tsangayar ilimin sharia na jami’ar Ahmadu Bello, inda ya yi jawabi a kan ‘Adana bayanan kwangila a mahangar shariar Musulunci: Yadda ake yi, ya aka yi shi a baya’.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel