Jihohi 5 kadai suka fara boyar mafi karancin albashin N30,000 - NLC

Jihohi 5 kadai suka fara boyar mafi karancin albashin N30,000 - NLC

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta bayyana cewa jihohi biyar kacal suka fara biyan ma'aikatansu mafi karancin albashin N30,000 watanni takwas bayan shugaban Buhari ya rattafa hannu kan dokar.

A jawabin da aka saki bayan ganawar masu ruwa da tsaki a Abuja, kungiyar kwadagon ta bayyana cewa jihohin Kaduna, Legas, Kebbi, Adamawa da Jigawa kadai ne suka fara biyan mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar kwadago NLC, Ayuba Wabba; sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, da shugaban majalisar yarjejniyar albashin ma'aikatan gwamnati, Abdulrafiu A. Adeniji.

NLC ta lissafo jihohin da ko kafa kwamitin biya basuyi ba a matsayin: Bauchi, Yobe, Rivers, Benue, Gombe, Kwara, Imo, Osun, Ekiti, Oyo, Anambra, Taraba, Cross River, Ogun, Enugu, Nasarawa, Plateau, Kogi da Delta.

Jawabin yace: "Ko wace jiha ta kira ganawar majalisar zantarwa na gaggawa da kuma taron dukkan ma'aikata domin sanar da su kan shawaran da masu ruwa da tsaki suka yanke da mafi karancin albashi."

"Jihohin da suka fara tattaunawar suyi hanzarin kammalawa nan da 31 ga Disamba, 2019."

"Jihohin da basu fara tattaunawa ba suyi gaggawan nada kwamitin yarjejeniya kuma su gaggauta gyaran albashin nan da 31 ga Disamba, 2019.

"Duk jihar da taki yin abubuwan nan da muka fada nan da 31 ga Disamba, 2019, zamu dauki mataki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel