Babu wanda yake ganin mutuncin mu, kowa nayi mana kallon azzalumai a Najeriya - Ahmad Lawan

Babu wanda yake ganin mutuncin mu, kowa nayi mana kallon azzalumai a Najeriya - Ahmad Lawan

- Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce, 'yan Najeriya na wa 'yan majalisa kallon mutanen banza ne

- Ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar a ranar Talata inda aka mika bukatar sauya sunan wata babbar makaranta a Daura

- Ya tabbatar da cewa, a wannan karon zasu ba 'yan Najeriya mamaki ta hanyar nuna musu shaidar wakilci nagari

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce, 'yan Najeriya na yi wa sanatoci kallon mutanen banza saboda basu fahimtarsu.

Shugaban majalisar dattijan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin jaddada cewa majalisar dattijan zata yi duk abinda ya dace don habaka yarda tsakaninta da 'yan Najeriya.

Wannan ya biyo bayan bukatar da Sanata Ahmed Babba Kaita ya mika gaban majalisar ta sauya sunan babbar makaranta ta Daura zuwa sunan marigayi Sanata Mustapha Bukar, wanda ya rasu.

A jawabinshi bayan karatun bukatar kashi na biyu, Lawan ya ce, "Dukkanmu da muka samu damar wata ma'amala da marigayi Bukar mun san yadda yake, jajircewarshi da sadaukarwa da yake ta alheri ce ga wannan majalisar.

KU KARANTA: Kaf Najeriya babu hanyar da tafi ta Kaduna zuwa Abuja tsaro a yanzu - El-Rufai

"Abu daya da za a yi don kwatanta alhairanshi, shine a mayar wa babbar makarantar da ke Daura sunanshi. Jama'ar Daura da duk wasu abokan aikinmu zasu yi farin cikin hakan. Wannan misali ne nagari kuma zai kawo nagarta."

A yayin tsokacin yadda 'yan Najeriya ke kallon 'yan majalisar, ya ce "Ana kallonmu a mutanen banza ne saboda mutane basu fahimtarmu duk da amanarsu suka bamu har suka zabemu. A wannan karon, zamuyi duk abinda ya dace don 'yan Najeriya su shaida kuma su san muna wakiltarsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel