El-Rufai yana daya daga cikin mutanen dana ji dadin aiki da su a lokacin mulkina - Obasanjo

El-Rufai yana daya daga cikin mutanen dana ji dadin aiki da su a lokacin mulkina - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kwatanta gwamnan jihar Kaduna da 'dan baiwa'

- Ya bayyana hakan ne a ziyarar ba zata da ya kaiwa gwamnan a ranar Laraba a garin Kaduna

- Obasanjo ya bayyana cewa, gwamnan na kwaikwayon salon shugabancinshi ne wanda ba ya ware mata

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kwatanta Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da 'dan baiwa' kuma mutum mai kwazo na ajin farko da za a iya aiki da.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ba zata da ya kai wa gwamnan a gidan gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba.

Idan zamu tuna, Malam Nasir ya rike ministan birnin tarayya a yayin mulkin shugaban kasa Obasanjo.

Obasanjo ya kwatanta gwamnan da 'dalibi nagari', ya kuma kwakwayi watsi da banbancin jinsi ne a yayin mulkin Obasanjo.

"Yana daya daga cikin mutane nagari da na yi aiki da; El-Rufai dan baiwa ne," Obasanjo yace.

"Muna da bukatar mutane irin shi. Mutumin da ka san yana tare da kai. Kuma zai iya duk aikin da ka saka shi.

"Ban ware mata a gwamnatina ba. Shima haka yayi a Kaduna. Dalibi ne nagari."

KU KARANTA: Babu wanda yake ganin mutuncin mu, kowa nayi mana kallon azzalumai a Najeriya - Ahmad Lawan

Obasanjo ya kwatanta ziyararshi a matsayin komawa gida, saboda "shima dan jihar ne". Ya bayyana cewa, ya gina gidanshi na farko a yankin Makera a tsakanin 1959 zuwa 1967 a lokacin da ya yi aiki a bataliyar Mogadishu ta sojin Najeriya a Kaduna.

Ya ce, wannan bataliyar ce ta farko da ta kunshi 'yan Najeriya daban-daban daga fadin kasar nan.

A mayar da martanin El-Rufai, ya kwatanta tsohon shugaban kasar a matsayin madubin dubawa. Ya kara da cewa, dabarun shugabancin da ya mallaka duk kwaikwayo ne daga madubin.

Ya mika godiya ga Obasanjo da ya samu lokacin kawo wannan ziyarar don ganin komai da idonshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel