Kaf Najeriya babu hanyar da tafi ta Kaduna zuwa Abuja tsaro a yanzu - El-Rufai

Kaf Najeriya babu hanyar da tafi ta Kaduna zuwa Abuja tsaro a yanzu - El-Rufai

- Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa a yanzu babu hanyar da ta kai ta Kaduna zuwa Abuja tsaro a fadin kasar nan

- Gwamnan ya ce, hakan ya biyo bayan kokarin gwamnatin jihar Kaduna wajen daukar tsautsauran matakin tsaro a hanyar

- Ya bayyana cewa, sama da watanni biyu da rabi, ba a kara garkuwa da mutane a kan hanyar ba

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa, a yanzu haka duk fadin Najeriya babu babbar hanya da ke da tsaron hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gidan rediyon Dabo FM ta jiyo gwamnan yana bayyana hakan ne bayan bude wani taro na hukumomin tsaro da aka gudanar a Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa, an kwashe watanni biyu da rabi ba a samu labarin yin garkuwa da wani a kan wannan hanyar ba. Hakan ya biyo matakan da gwamnati ke ci gaba da dauka ne.

El-Rufai ya bayyana cewa: "Hanyar Kaduna zuwa Abuja a yanzu ta fi kowacce hanya tsaro a Najeriya. Hakan ya biyo bayan jiragen sama na sojojin sama da ke aiki a wannan hanya. Jiragen na samar da bayanai."

KU KARANTA: An kone wani saurayi kurmus, bayan ya daddatsa mutane 9 da adda, inda 7 daga cikin 'yan uwanshi ne na jini

Sai dai kuma ya kara da cewa: "Amma har yanzu mutane na jin tsoron bin wannan hanya."

"A halin yanzu kusan duk masu garkuwa da mutane da ke gefen hanyar an tarwatsa su ko kuma an kora su cikin jeji," in ji shi.

Ya ce, ko da yake ana cigaba da yin garkuwa da mutane a jihar, amma bai yi muni kamar yadda ake yi a baya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel