Da duminsa: Ministan Shari'a ya umurci DSS ta dakatad da lamarin gurfanar da Sowore

Da duminsa: Ministan Shari'a ya umurci DSS ta dakatad da lamarin gurfanar da Sowore

- Minista Abubakar Malami ya umurci hukumar DSS ta mika masa takardun zargin Omoyele Sowore

- A wasikar da ta aikawa hukumar, ya ce akwai bukar duba dalilin da yasa ake tsare matashin

Babban lauyan tarayya kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya umurci hukumar tsaron farin kaya wato DSS ta dakatad da shari'ar dan jarida, Omoyele Sowore, a kotu.

Wannan umurni ya biyo bayan korafe-korafen masu fada a ji a Najeriya da kasashen wajen kan sake damke Omoyele Sowore da hukumar DSS tayi a babban kotun tarayya dake Abuja ranar juma'ar da ya gabata.

Malami a bukaci DSS ta kawo masa dukkan takardun zargi da tuhumce-tuhumcen da take yiwa Sowore da gaggawa.

Hakazalika ministan ya bukaci an gaggauta kammala bincike kan lamarin harin da jami'an DSS suka kaiwa Sowore cikin kotu domin damkeshi.

A jawabin mai magana da yawun Malami, Jibliru Gwandu, ya saki, yace ministan shari'a na duakan wannan mataki ne domin bincike kan korafe-korafen da ake yi tattare da tsare Omoyele Sowore.

A bangare guda, Fadar shugaban kasan Najeriya a ranar Laraba ta gargadi kasar Amurka, Birtaniya da gamayyar kasashen Turai da su shiga taitayinsu kuma su daina shisshigi cikin lamarin Najeriya, musamman abinda ya shafi take haddin bil adama.

Fadar ta yi gargadin ne ta bakin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, Femi Adesina, yayinda yake martani kan rahotannin cewa kasar Amurka da Birtaniyya sunce ana yawan take hakkin bil adama a Najeriya musamman kan lamarin Omoyele Sowore

Ya yi martanin cewa hirar da yayi da tashar Channels ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel