Yanzu-yanzu: An dakatad da ayyukan kamfanin jirgin 'Turkish Air' a Najeriya

Yanzu-yanzu: An dakatad da ayyukan kamfanin jirgin 'Turkish Air' a Najeriya

Hukumar harkokin jiragen saman Najeriya NCAA ta dakatad da kamfanin jirgin kasar Turkiyya, Turkish Air, daga aiki a Najeriya bisa koke-koken fasinjoji kan jinkirin kawo jakunkunansu.

Wannan dakatarwa zai kaddama ne ranar 16 ga watan Disamba, 2019.

Hukumar ta ce za'a dakatad da kamfanin jirgin har sai lokacin da kamfanin ta shirya samun babban jirgin da zai iya daukan fasinjoji da kayayyakinsu a lokaci daya.

A wasikar da NCAA ta aikawa manajan kamfanin jirgin, GC Abdullahi Sidi, ya ce tsawon makonni biyu kenan ana samun matsalan rike kayayyakin mutane.

A wasikar, ya bayyana cewa jinkiri wajen kawo jakunkunan matafiya yana kawo matsala saboda jirgin iso Najeriya ba tare yawancin kayayyakin mutane ba.

Yace: Hukumar harkokin jiragen saman Najeriya NCAA tana nuna bacin ranta kan matsalolin da ake samu na rashin kawo fasinjoji da jakunkunansu a lokaci guda."

"Makonni biyu kenan ana samun wannan matsalan kuma abin ya tsananta kwanakin nan inda jirgi ya sauka ba tare da kayayyakin kashi 85% na fasinjoji."

A wani labarin daban, wani fasinjar jirgin sama mai suna, Jude Oladapo, ya yanke jiki ya mutu yayinda yake shirin shiga jirgi a babban filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Lagos.

Kakakin ofishin hukumar yan sandan na filin jirgin saman, DSP Joseph Alabi, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai ranar Lahadi a Legas.

DSP Joseph Alabi ya ce fasinjan wanda ya nufi shiga jirgin Air France ya yanke jiki ya fadi ne bayan samun labarin mutuwar matarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel