Mun damu da kama Sowore da aka sake yi – inji Sanata Chris Coons

Mun damu da kama Sowore da aka sake yi – inji Sanata Chris Coons

Sanata Christopher Andrew Coons ya fito ya yi magana da babbar murya bayan jami’an tsaro sun sake yin ram da fitaccen ‘Dan gwarmayan nan kuma ‘Dan siyasa watau Omoyele Sowore.

Sanatan mai wakiltar Yankin Delaware a kasar Amurka tun shekarar 2010, ya nuna damuwarsa ainun a shafinsa na Tuwita. Wannan sako ya samu karbuwa wurin dubban mutane a dandalin.

“Na yi matuka damuwa gane da yadda ake cigaba da taso ‘Dan gwagwarmaya, ‘Dan jarida kuma ‘dan takarar shugaban kasar Najeriya, Omoyele Sowore.”

“Ina kira ga Jami’an tsaron Najeriya su bi doka da tsarin mulki, su fito da Sowore kamar yadda belinsa ya ce, sannan ayi bincike a kan sake kama shi.”

KU KARANTA: Sai an dage wajen yaki da rashin gaskiya a Najeriya – Jega

‘Dan Majalisar dattawan na Amurka ya kuma kara da cewa: “Wannan lamari ya na nuna yadda ake kokarin kakabawa ‘Yan Najeriya takunkumi.”

"Jinjinawa Masu gwargwarmaya da kokarin kare hakkin ‘Yan Adama ya kamata a rika yi a Najeriya da sauran kasashen Duniya, ba bi ta kansu ba."

Chris Coons ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Tuwita a Ranar 10 ga Watan Disamban 2019. Wannan ya na zuwa ne kwanaki hudu bayan jami’an DSS sun sake kama Yele Sowore a kotu.

Kawo yanzu gwamnatin tarayya ta bakin Ministan shari’a, Abubakar Malami, ta tabbatar da cewa za ta gudanar da bincike a kan lamarin. Jami’an DSS sun fitar da jawabi a kan abin da ya faru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel