Babu wata rigima tsakanin Buhari da Osinbajo – APC ta reshen Kudu maso Yamma

Babu wata rigima tsakanin Buhari da Osinbajo – APC ta reshen Kudu maso Yamma

Jam’iyyar APC ta reshen Kudu maso Yammacin Najeriya da kuma ta bangaren babban birnin tarayya Abuja, sun yi watsi da rade-radin da ke yawo na rikici a fadar shugaban kasa Buhari.

‘Ya ‘yan Jam’iyyar mai mulki sun musanya cewa ba a samu wani sartse wajen aiki tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakinsa watau Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Shugaban kungiyar, Fasto Olusegun Erinle shi ne ya yi wannan jawabi a Ranar Alhamis 12 ga Watan Disamban 2019. Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta kawo wannan rahoto Ranar Juma’a.

Olusegun Erinle ya yi wa Manema labarai jawabi a Garin Abuja, ya na mai cewa tun daga lokacin da shugabannin kasar su ka ci zabe a shekarar 2015, su ke aiki ba tare da an samu matsala ba.

Fasto Erinle ya gargadi masu kokarin nunawa Duniya cewa rikici ya shiga tsakanin shugabannin tare da kiransu su tuba. Shugaban jam’iyyar ya ce wasu ne kawai su ke kitsa wannan karyayyaki.

KU KARANTA: Wasu bata-gari sun karbe kasar nan daga hannun Mai gida na - Aisha Buhari

Babu wata rigima tsakanin Buhari da Osinbajo – APC ta reshen Kudu maso Yamma

Kungiyar Yarbawa ta ce Buhari da Osinbajo su na nan yadda aka san su
Source: Twitter

Jagoran jam’iyyar ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su dafawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen cika alkawuran da ta dauka, a maimakon karkatar da hankalinsu kan zargin wani rikici.

“Lokaci ya yi da za mu fito a matsayin mu na APC ta reshen Kudu maso Yamma da Birnin Tarayya, mu yi wa jama’a bayani a game da rade-radin da ke yawo game da samun sabani wajen aiki tsakanin Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Osinbajo, kafin kowa ya dauka,.”

‘Tun daga lokacin da aka rantsar da wannan gwamnati a 2015, tafiyar canji ta kawo mana sauyi na tattalin arziki da cigaban kasa, sannan kuma an ga yadda ake aiki hannu-da-hannu tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa, fiye da yadda aka saba gani a gwamnatocin da aka yi a baya.”

Erinle ya ce: “Shugaban kasar ya saba jaddada irin yaddar da ya yi wa mataimakinsa. Ka da mutane su nemi nunawa Duniya cewa akwai rikici tsakaninsu. Babu wata rigima da ta ratsa su”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel