Ta debo da zafi: Bazan iya aurar mutumin da bashi da akalla motoci 3, gidaje 2 da kuma tsayyen kasuwanci ba - Budurwa

Ta debo da zafi: Bazan iya aurar mutumin da bashi da akalla motoci 3, gidaje 2 da kuma tsayyen kasuwanci ba - Budurwa

- Batun rashin mazan aure da mata ke fama dashi da kuma son abun duniya na matan ya kasance abun tattaunawa kullum a kafafen sada zumunta

- Jarumar BBNaija ta 2018, Khloe ta bayyana cewa, ba za ta iya auran miji mara motoci 3 ba, gidaje biyu da kasuwanci biyu tsayayyu

- Dalilinta na fadin haka kuwa ta ce saboda ita da ‘yan uwanta sun sha wahalar rayuwa sosai ne a lokacin da suka girma

Batun cewa mata basu son auren mazan da basu da kudi ya zama abun tattaunawa a zamanin nan. An kassance ana tattauna wannan batun kusan koyaushe a kafafen sada zumuntar zamani, duba da yadda matan zamanin nan ke ikirarin basu samun mazan aure.

Babu shakka, kowa yana son yin rayuwa mai kyau. Koda kuwa kowa ya san cewa talauci na haifar da matsin rayuwa. Sau da yawa, mazan da basu da abun hannu basu cika samun kyawawan mata ba don su aura, saboda mawadatan sukan sha gabansu wajen neman auren kyawawan.

Tauraruwar wasan nan na BBnaija na 2018, Khloe, a cikin kwanakin nan ta tatauna a shafinta na Instagram game da mutumin da take so ya zama dan uwan rayuwarta.

Kamar yadda tauraruwar tace, ba zata iya auran mutumin da bashi da motoci a kalla uku ba, gidaje biyu da kasuwanci nau’ika biyu tsayayyu.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Ni mijin ta ce ne, sai abinda matata ta ce nake yi - Cewar Ado Gwanja

A yayin da take karin haske, Khloe ta ce ita da ‘yan uwanta sun sha wahala sosai a lokacin da suka girma, kuma ba za ta so ta kawo yara wannan duniyar ba idan ita da mijinta ba zasu kula da su ba.

Yayin da take magana a kan koma bayan ra’ayinta, Khloe ta ce rayuwarta kenan kuma ita ta zabi hakan.

Ta kuma karfafa wasu da su sanya nasu ra’ayin. Ta rubuta: “Ba zan iya auran mutumin da bashi da wadata ba. Wanda bashi da motoci 3, gidaje 2 da kasuwanci kwarara 2 ba. Saboda haka ne mutane ke ta zagina a soshiyal midiya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel