Kotu ta bayar da umurnin a damko Diezani nan take

Kotu ta bayar da umurnin a damko Diezani nan take

- Wata babban kotu da ke zamanta a Adamawa ta bayar da umurnin kamo tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke

- Alkalin kotun, Nathan Musa, ya bayar da umurnin ne yayin da ya ke yanke hukunci aike wa da wasu jami'an INEC biyu da suka karbi cin hanci daga hannun Alison-Madueke gidan yari

- Musa ya umurci rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi aiki tare da 'yan sandan kasa da kasa (interpol) ta kamo Diezani Alison-Madueke

Wata babban kotu da ke Adamawa ta umurci sufeta janar na 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu ya kamo tsohuwar ministan albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke saboda samunta da aka yi na bayar da cin hanci na naira miliyan N362 ga wasu jami'an INEC biyu yayin zaben shugaban kasa na 2015.

The Cable ruwaito cewa alkalin kotun, Nathan Musa, ya bayar da umurnin kamo tsohuwar ministan a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba ne yayin da ya yanke hukuncin aike wa da wasu jami'an INEC biyu gidan yari saboda karbar cin hanci daga hannun Diezani.

DUBA WANNAN: Me yayi zafi? Amarya ta fada rijiya ana gobe bikinta a jihar Kano

Kotun ta umurci rundunar 'yan sandan Najeriya ta hada kai da 'yan sandan kasa da kasa Interol ta kamo tsohuwar ministan don ta fuskanci shari'a.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa wata babban kotu a Yola ta aike da wasu ma'aikatan INEC biyu gidan yari na shekaru 42 bayan an same su da laifin karbar rashawa.

Kotun ta bayar da hukuncin ne karkashin jagorancin Mai shari'a Nathan Musa a ranar Alhamis 12 ga watan Disamba.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da hukumar yaki da rashawa EFCC ta shigar a kansu.

Mai shari'a Musa ya ce ma'aikacin INEC, Ibrahim Mohammed Umar da Sahabo Iya Hamman za su yi zaman gidan yari na shekaru bakwai kowannensu sakamakon laifuka uku da aka same su da aikatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel