Kotu ta bada umurnin ajiye jigo a APC a gidan yari kan yi wa gwamnan PDP kazafi

Kotu ta bada umurnin ajiye jigo a APC a gidan yari kan yi wa gwamnan PDP kazafi

- Kotun Majistare da ke Bauchi ta bayar da umurnin a ajiye Umar Mohammed Mai Fata a gidan yari

- Kotun ta bayar da umurnin ne bayan lauya mai kare Mohammed Mai Fata ya fice daga kotu ana cikin shari'a ya kuma kwashe kimanin mintuna 30 bai dawo ba

- Kotun ta bayar da umurnin ajiye jigon na APC a gidan yari ne bayan gwamnatin jihar ta maka shi kara a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa gwamna Bala Mohammed ya kashe N1bn na jihar a zaben Bayelsa

Kotun Majistare da ke Bauchi ta bayar da umurnin tsare jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, Umar Mohammed Mai Fata a gidan gyaran hali kan kazafi da ya yi wa gwamna Bala Mohammed na kashe naira biliyan daya daga asusun gwamnati don zaben jihar Bayelsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Damfara: Amurka ta kwace jirgin saman wani attajirin dan Najeriya

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Ayuba Danladi da ya shigar da karar a madadin kwamishinan 'yan sanda na jihar ya shaida wa kotu cewa Mai Fata a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo ya yi ikirarin cewa gwamna Mohammed ya dauki naira biliyan daya daga asusun gwamnatin jihar Bauchi domin amfani da shi a zaben gwamnan jihar Bayelsa inda aka nada shi shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan PDP a jihar Bayelsa.

Sai dai bayan kimanin mintuna 30 da lauyan wanda aka yi karar ya fita daga kotu kuma bai dawo ba, mai shigar da karar ya bukaci kotu da dage cigaba da karar har zuwa lokacin da lauyan wanda aka yi karar ya shirya a cigaba da shari'ar.

A bangarenta, alkaliyar kotun ta Majistaren, Safiya Doma ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Disamban 2019 kuma ta bayar da umurnin a bawa wanda ake zargin masauki a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a cigaba da zaman sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel