IGP: An kama mutane 49 a kan rikicin zaben Gwamnan Jihohin Kogi da Bayelsa

IGP: An kama mutane 49 a kan rikicin zaben Gwamnan Jihohin Kogi da Bayelsa

Sufeta Janar ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa sun damke mutane 49 bisa zargin cewa akwai hannunsu wajen tada rikicin da aka yi a zabukan jihar Bayelsa da Kogi.

IGP Mohammed Adamu, ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron da aka shirya na tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya a Ranar Laraba 11 ga Watan Disamban 2019 a Garin Abuja.

Wani babban jami’in ‘Yan Sandan Najeriya watau AIG, Bashir Makama, shi ne ya wakilci IGP Mohammed Adamu a wajen wannan taro. An gudanar da taron ne a babbar Hedikwatar INEC.

A cewar AIG Bashir Makama, mutane 35 ne aka cafke a jihar Bayelsa, wannan ya na nufin an kama sauran mutane 14 ne a jihar Kogi a zaben gwamnan da aka yi Ranar 16 ga Watan Nuwamba.

A game da zaben Bayelsa, Dakaru 31, 041 aka tura zuwa jihar mai arzikin man fetur domin wannan aiki, wanda bayan wannan aka samu matsalar hayaniya a lokacin.”

KU KARANTA: Kudin Barayi N600m, $700m sun shiga hannun mu a Kano – EFCC

“Adadin mutanen da aka kama da laifin tada rikicin zabe ya kai 35, yanzu haka ana binciken su a babban ofishin ‘Yan Sanda da ke Garin Benin."

AIG Makama a madadin Sufeta Janar ya kara da cewa: “Mutum 8 kadai aka iya kamawa da laifin tada zaune tsaye a lokacin zaben jihar Kogi.”

Shugaban ‘Yan Sandan kasar ya na zargin wadannan mutane da laifin kawo hatsaniyar siyasa. IGP ya ke cewa duk da kalubalen da ake fuskanta na rikicin, akwai damar gyara sha’anin zabe.

“Haka game da Jagorar jam’iyyar PDP da aka kona har lahira a gidanta a Kogi, an kama mutane shida a mabanbantan lokaci, kawo yanzu ba a kammala bincike ba tukuna.”

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Manjo Janar Mohammed Babagana Monguno (mai ritaya), ya halarci taron inda ya bada shawarwari. Sanusi Galadima shi ne ya wakilce sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel