Yanzu-yanzu: IG na 'yan sanda ya dakatar da gangamin taron da APC ta shirya a Edo

Yanzu-yanzu: IG na 'yan sanda ya dakatar da gangamin taron da APC ta shirya a Edo

Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya dakatar da wata gangamin taron da wani bangare na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da shirya yi a Benin, jihar Edo, a ranar Juma'a.

Bangaren da ta shirya taron ita ce wadda ke biyaya ga shugaban jam'iyyar ta APC na kasa, Adams Oshimhole kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A jawabin da ya yi yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, Philip Shuaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya ce ya samu wasikar dakatar da taron gangamin misalin karfe 5 na yamma daga headkwatan 'yan sanda.

Ya ce ya fadawa sufeta janar na 'yan sanda cewa ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar wadanda za su hallarci taron ba.

A cewar Shuaibu, taron kawai 'wani salo ne na tayar da zaune tsaye.'

DUBA WANNAN: Damfara: Amurka ta kwace jirgin saman wani attajirin dan Najeriya

Ya ce, abin takaici ne yadda Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar na kasa da ya dauka a matsayin mahaifinsa ke jagorantar kawo rashin jituwa da rabuwar kai a jam'iyyar.

Ya ce an dakatar da Oshiomhole daga jam'iyyar a jihar saboda haka ba shi da ta cewa kan yadda suke gudanar da harkokinsu.

A baya, sufeta janar na 'yan sandan ya bawa jam'iyyar ta APC ikon yin taron don tarbar Ize Iyamu amma gwamnan jihar Godwin Obaseki ya ce bai san da batun wani taron APC a jihar ba.

Anselm Ojezua, shugaban jam'iyyar APC na jihar, shi ma ya ce shugabannin jam'iyyar na jihar ba su san da taron ba kuma ya bukaci 'ya'yan jam'iyyar na jihar su yi watsi da taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel