APC vs PDP: Oshiomhole da Secondus sunyi musayar kalamai kan da zabe

APC vs PDP: Oshiomhole da Secondus sunyi musayar kalamai kan da zabe

Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya a ranar Talata sun yi musayar kalmomi a kan halin da kasar ke ciki kuma suka yi wasa da dariya da juna yayin kaddamar da wani litafi a birnin tarayya Abuja.

Sun yi musayar kalaman ne a kan mutunta hakokin dan adam da yadda ake gudanar da zabe musamman zaben gwamna na jihar Kogi karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na APC da kuma gwamnatocin PDP daga 1999 zuwa 2015.

Lamarin ya faru ne yayin kaddamar da litafin da Eric Osagie, tsohon babban manajan jaridar The Sun ya rubuta mai taken 'The Big Interviews: How to get the news subjects and angles that make the headlines'.

Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole ne dauki hankulan mutane bayan ya shigo dakin taron kuma ya garzaya wurin takwararsa na PDP, Uche Secondus ya rungume shi kuma suka yi wasa da dariya kuma ya maimaita hakan da gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike.

DUBA WANNAN: Damfara: Amurka ta kwace jirgin saman wani attajirin dan Najeriya

A yayin da aka kira shi ya yi jawabi, Oshiomhole ne ya fara zargin jam'iyyar na PDP da cewa bata aikata abubuwan da ke kira a aikata ba a cikin shekaru 16 da ta kwashe tana mulkar kasar.

Oshiomhole ya yi jawabi kan abubuwan da gwamnati APC ta aikata inda ya zargi wani tsohon gwamnan PDP da fita kasashen waje yana wa'azi kan abubuwan da shi baya aikatawa.

Sai dai jam'iyyar ta PDP ta bakin Secondus ta Wike sun mayar masa martani. Sun ce har yanzu abubuwa ba su canja zani ba a kasar tun 2015 da jam'iyyar APC ta karbi mulki.

Oshiomhole ya bayar da misalin lokuta biyu da tsohon shugaban kasa na gwamnatin PDP ya fito a wata hirar talabijin yana shawartar mutane su aikata abubuwan da shi baya aikata.

Oshiomhole ya ce, "Na kalli hirar da aka yi da shi a kasar waje da tsohon shugaban kasan Najeriya (amma ba zan fadi sunansa ba sai dai Wike ya san shi kuma har yanzu suna harka) inda aka yi masa muhimman tambayoyi biyu.

"Yana ta bayar da amsoshi kuma ya ce yawan al'umma shine matsalar Afrika. Ya ce yawan al'ummar Afrika na kasuwa da 3% shi yasa talauci ya yi wa nahiyar katutu kuma ya ce dole sai an dauki mataki kan yawan al'umma kafin a warware matsalolin Afirka.

"Daga nan dan jaridar ya ce masa kamata ya yi ka auri mata daya kuma ka haifi yara daya ko biyu domin ka yi misali kan kanka."

A bangarensa, shugaban na PDP ya ce babu abinda ya canja a kasar tun 2015 da gwamnatin APC ta karbi mulki.

"Tun daga lokacin da jam'iyyar adawa ta karbi mulki, mun ga wani cigaba ne, na san ka san amsar.

"Abinda ya fi muhimmanci ma, ana barin mu muyi magana ne yanzu? Ko a zamanin mulkin sojoji 'yan jarida suna iya magana kuma suna fafutikan kare hakokinsu. Amma mun ga kudirorin doka a majalisar tarayya na neman hana mutane fadin albarkacin bakinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel