Buhari ya bayyana alhininsa da mutuwar Sojoji 63 a hannun yan ta’adda

Buhari ya bayyana alhininsa da mutuwar Sojoji 63 a hannun yan ta’adda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma gwamnatin kasar Nijar, tare da bayyana alhininsa bisa kisan da wasu gungun yan ta’adda suka yi ma dakarun Sojojin kasar Nijar guda 63 a garin Inates dake iyaka da kasar Mali.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, inda yace yan ta’addan sun fito ne daga kasar Mali, suka Nijar inda suka kashe Sojoji 63, ba’a san inda 34 suka shiga ba.

KU KARANTA: Yan Najeriya 4 sun shiga hannu a kasar Amuka kan satar naira biliyan 6.5

Buhari ya jaddada manufarsa na ganin ya kawo karshen ayyukan yan ta’adda a Najeriya da ma nahiyar Afirka gaba daya ta hanyar aikin hadin gwiwa da sauran kasashe dake makwabtaka da Najeriya, da kuma manyan kasashen duniya da kungiyoyi masu zaman kansu.

“A madadina, gwamnatin Najeriya da kuma jama’an Najeriya, ina mika ta’aziyyata ga iyalan mamatan, gwamnatin kasar Nijar da al’ummar kasar Nijar biyo bayan wannan harin ta’addanci. Muna addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu, Ya kuma bayyana wadanda suka bata.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Sojin Najeriya ta bayyana kungiyar tsagerun IPOB dake rajin kafa kasar Biyafara da taimakawa wajen nuna gazawar Sojojin Najeriya a yakin da take yi da kungiyar ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar inda yace wani bidiyon dake nuna yadda yan Boko Haram suka yi ma wasu Sojojin Najeriya kisan gilla ba daga Boko Haram ya fito ba, IPOB ne suka harhada bidiyon.

Sagir yana mayar da martani ne game da wani bidiyo da aka yi ikirarin mayakan Boko Haram ne a cikinsa suke kashe wasu Sojojin Najeriya guda uku, wadanda suka tsugunar dasu, suka sanyasu amsa laifukansu, sa’annan suka kashesu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel