Badakalar zaben 2015: Kotu ta yankewa jami'an INEC 2 hukuncin shekaru 42 a gidan gyara hali

Badakalar zaben 2015: Kotu ta yankewa jami'an INEC 2 hukuncin shekaru 42 a gidan gyara hali

A ranar Alhamis, Wata babbar kotu dake zamanta a Yola, karkashin jagorancin Alkali Nathan Musa, ta yanke hukuncin jefa wasu jami'an hukumar gudanar da zaben kasa INEC gidan gyara hali na tsawon shekaru 42 kan laifin amsan cin hanci.

Hakazalika Jastis Musa ya yi kira ga sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, da hukumar yan sandan duniya Interpol, sn damko tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke, domin ta fuskanci ukubar baiwa jami'an INEC din cin hancin N362 miliyan na magudin zaben 2015.

An biya wadannan jami'an ne domin su murde zaben shugaban kasa tsakanin Goodluck Jonathan da shugaba Muhammadu Buhari.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta shigar da Mohammed Umar da Shabo Iya Hamman kotu kotu ne bayan asirinsu ya tonu cewa sun karbi cin hanci hannun tsohuwar ministar man fetur.

DUBA NAN Rikici na Yari, babu gudu, babu ja da baya - Kabiru Marafa

Alkalin ya ce bayan tabbatar da hujjojin da aka kawo kan munkaran, kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai-bakwai kan laifuka uku da ake zarginsu da shi.

Amma tunda wannan shine karo na farko da zasu aikata laifi, kotu ta daga musu kafa suyi shekaru bakwai.

"Wannan laifin na da ukuba na doka, babu yadda zanyi. An yanke musu hukuncin shekari bakwai kuma babu fansa."

"Amma tunda an nemi alfarma, na amince suyi shekaru bakwai-bakwan a jere."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel