Rikici na Yari, babu gudu, babu ja da baya - Kabiru Marafa

Rikici na Yari, babu gudu, babu ja da baya - Kabiru Marafa

Babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya nisanta kansa daga rahoton cewa an yi zaman sulhu tsakanin yan bangarensa da tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari.

Za ku tuna cewa kakakin bangaren Yari na jam'iyyar APC a jihar, Shehu Isah, ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya gana da wasu mambobin bangaren Kabiru Marafa domin dinke barakar da ke tsakaninsu.

Wannan rikici ya sabbabawa jam'iyyar biyu babu a zaben bara inda kotu ta mikawa jam'iyyar PDP mulki bulus.

A martani Marafa kan rahoton, ya ce bashi da masaniya game da zaman sulhun da ake radawa.

Yace: "Babu wanda ya sanar da ni kuma babu wani ya tuntubeni kan wani zaman sulhu domin dinke barakar APC a jihar Zamfara."

"Shi (Yari) yayi watsi da dukkan yunkurin da uwar jam'iyya, fadar shugaban kasa, abokan siyasa da abokan arzikin sukayi na sulhu da zaman lafiya saboda yana ji da dukiyar jiha, giyar mulki da karfin kungiyar gwamnoni dake karkashinsa."

"Ya dogara kan shari'ar kotun jihar kuma kotun daukaka kara da na Koli sun yi watsi da ita."

"Yanzu da ya sauka daga mulki kuma babu jama'a, yana kokarin shirya wata ganawar sulhu domin kara dawo da kansa."

"Ni mai biyayya ne ga jam'iyyar APC a sama da kasa, babu gudu, babu ja da baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel