Zargin take hakkin bil Adama: Ku shiga taitayinku - Fadar shugaban kasa ta gargadi Amurka, Ingila da EU

Zargin take hakkin bil Adama: Ku shiga taitayinku - Fadar shugaban kasa ta gargadi Amurka, Ingila da EU

Fadar shugaban kasan Najeriya a ranar Laraba ta gargadi kasar Amurka, Birtaniya da gamayyar kasashen Turai da su shiga taitayinsu kuma su daina shisshigi cikin lamarin Najeriya, musamman abinda ya shafi take haddin bil adama.

Fadar ta yi gargadin ne ta bakin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, Femi Adesina, yayinda yake martani kan rahotannin cewa kasar Amurka da Birtaniyya sunce ana yawan take hakkin bil adama a Najeriya.

Ya yi martanin cewa hirar da yayi da tashar Channels ranar Laraba.

Mista Adesina ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai yanci kuma ba za ta damu da babatun wasu kasashen ketare ba.

Yayinda yake martani kan kan harin da jami'an tsaron farin kaya DSS suka kai kotu domin sake damke mai kira ga juyin juya hali, Omoyele Sowore, yace: "Najeriya ba ta karkashin Amurka, Birtaniya ko gammayar kasashen Turai."

"Najeriya kasa ce mai yanci. Wadannan kasashen na da nasu matsalolin. Su mayar da hankali kan matsalolinsu. Su bar Najeriya ta magance matsalolinta na cikin gida. Mu ba yaransu bane."

A bangare guda, ranar Laraba, 11 ga watan Disamba 2019, uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ya saki bama-bamai kalamai kan mai magana da yawun mijinta, Malam Garba Shehu.

A jawabin da ta saki, ta yi gargadi ga Garba Shehu inda tace ba zata sake lamuntan rainin wayon da yake yi mata ba.

Legit.ng ta tattaro muku a takaicen takaitawa, korafe-korafe bakwai da Aisha ke yiwa hadimin mijinta, Malam Garba Shehu.

DUBA NAN Korafe-korafe 7 da Aisha Buhari tayi kan Garba Shehu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel