Kura ta kai bango: Zamu fara zanga-zanga idan har bamu samu mazajen aure ba cikin shekarar nan - Kungiyar likitoci mata

Kura ta kai bango: Zamu fara zanga-zanga idan har bamu samu mazajen aure ba cikin shekarar nan - Kungiyar likitoci mata

- A watannin da suka gabata ne, ma'aikatan jinyar kasar Ghana suka koka a kan rashin aurensu

- A halin yanzu, sunce zasu fito zanga-zanga matukar wannan shekara ta kare basu samu maza ba

- Sun fitar da shafinsu na yanar gizo don nemansu tare da aurensu

A watannin da suka gabata, an ruwaito yadda ma'aikatan jinyar kasar Ghana suka koka kan wuyar samun mazan aure.

Kamar yadda suka ce, suna da rufin asiri da abun hannunsu amma suna fuskantar matsananciyar wahala wajen samun abokan rayuwa.

Da matsi tare da takura daga dangi, wani sashi na ma'aikatan jinyar sun yi barazanar fita zanga-zanga matukar basu samu mazan aure ba zuwa karshen wannan shekarar.

Abun cike da mamaki da al'ajabi, amma wadannan kyawawan ma'aikatan jinyar sun tabbatar da zasu fito zanga-zanga, yayin tattaunawa da aka yi dasu cikin kwanakin nan.

KU KARANTA: Garba Shehu fuska biyu gareshi, saboda haka lokaci yayi da zai ajiye aikinsa - Aisha Buhari

Kamar yadda daya daga cikin ma'aikatan jinyar ta sanar, ta yi mamakin yadda suka sanar a watannin baya amma babu namijin da ya dage ya tunkarosu. Don haka, ba shakka zasu fito zanga-zanga.

"Muna cikin damuwa mai tsanani saboda bamu san dalilin da yasa mazan Ghana suka ki aurenmu ba. Muna da kyau kuma akwai kudi tare damu. Idan ba a yi komai a kai ba, zamu fito zanga-zanga don nuna fusatarmu. Zai fi kyau idan aka fito aka auremu." Ta ce.

A hakan dai, sun fitar da shafinsu na yanar gizo ga mai bukata, don nemansu da aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel