Hukuncin da kotu ta yanke bai da alaka da kafa sabbin masarautu - Ganduje

Hukuncin da kotu ta yanke bai da alaka da kafa sabbin masarautu - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano tace hukuncin babbar kotun jihar kan sabuwar majalisar sarakuna bai da alaka da kafa sabbin masarautu hudu da gwamnan yayi.

Jawabin da ministan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, ya saki ya bayyana cewa wasu masu adawa da sabbin masarautun ne ke yada jita-jitan cewa kotu ta soke masarautu.

Jawabin ya kara da cewa yan adawan za su sha mamaki idan kotu ta yanke hukunci kan lamarin sabbin masarautun.

Malam Muhammad Garba ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta samu nasara a kotu saboda ta bi tsarin doka wajnnan karon.

Ya yi kira da al'ummar jihar su kwantar da hankulansu kuma su kasance masu biyayya ga doka idan kotu ta yanke hukunci.

A wani labarin daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ba kwamishinan aiyuka da habaka ababen more rayuwa, Injiniya Mu’azu Magaji, umarnin gyaran ofishin majalisar sarakuna, Gidan Shettima, wanda yake a farfajiyar fadar Sarkin Kano.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, yin hakan na daga cikin shirye-shiryen kafa majalisar sarakunan a jihar Kano.

A wata takarda da babban sakataren yada labarai na Gwamna ya fitar a ranar Alhamis, Abba Anwar ya bayyana cewa, wannan umarnin alamu ne dake nuna cewa, rantsar da sarakunan za a yi shi nan ba da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel