Furucin Aisha: Ta tabbata ba Buhari ke mulkin Najeriya ba – jam’iyyar PDP

Furucin Aisha: Ta tabbata ba Buhari ke mulkin Najeriya ba – jam’iyyar PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa kalaman da Aisha Buhari ta furta a yan kwanakin nan game da rikicin dake cikin fadar shugaban kasa ya tabbatar da cewa ba Buhari ke mulkin Najeriya ba, wasu shafaffu sun kwace mulki a hannunsa.

PDP ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan, a ranar Laraba, inda yace maganganun da Aisha ke yi gaskiya ne, kuma hakan ya nuna gazawar shugaban kasa Buhari game da iya shugabanci.

KU KARANTA: Bidiyon kashe Sojojin Najeriya: Kungiyar IPOB tana taimaka ma Boko Haram – kaakakin Soja

“Maganan da Aisha ta yi na cewa wasu mutane sun amshe ragamar iko a fadar gwamnatin Najeriya inda har suke daukan mataki tare da yanke hukunci ba tare da sun tuntubeshi bay a nuna mutanen nan sun kwace mulki daga hannun Buhari.

“Don haka a maimakon Buhari ya yi aikinsa na mulkin Najeriya, ya mayar da mulki wasan yara, wannan shi ne dalilin da yasa abubuwa ba zasu gyaru a Najeriya ba, sai dai su cigaba da tabarbarewa.

"Ta tabbata gwamnatin Buhari abin kunya ne ga yan Najeriya, saboda a tarihin Najeriya ba’a taba samun lokacin da aka banzatar da gwamnati ba kamar a wannan lokaci ba.” Inji shi.

Daga karshe jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugaba Buhari daya gyara gidansa domin ya tseratar da Najeriya da cigaba da jin kunya a idon duniya.

Idan za’a tuna uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta saki bama-baman kalamai kan mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, inda ta zarge shi da rashin kare Buhari yadda ya kamata

Hakazalika Aisha ta labarta cewa lokacin da aka shirya kaidin bidiyon da diyar Mamman Daura ta yada a yanar gizo inda ake kokarin fahimtar da yan Najeriya cewa an hanata shiga fadar shugaban kasa lokacin da ta dawo Najeriya bayan dogon hutun da ta dauka, Garba Shehu yayi shiru duk da cewa ya san gaskiyar lamarin maimakon karyata labarin.

Bugu da kari lokacin da ake rade-radin cewa Buhari zai kara aure, Aisha ta ce Garba Shehu ya sake shiru amma yayi gaggawan sakin jawabi lokacin da ya samu labarin cewa za ta dawo gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel