Bidiyon kashe Sojojin Najeriya: Kungiyar IPOB tana taimaka ma Boko Haram – kaakakin Soja

Bidiyon kashe Sojojin Najeriya: Kungiyar IPOB tana taimaka ma Boko Haram – kaakakin Soja

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana kungiyar tsagerun IPOB dake rajin kafa kasar Biyafara da taimakawa wajen nuna gazawar Sojojin Najeriya a yakin da take yi da kungiyar ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar inda yace wani bidiyon dake nuna yadda yan Boko Haram suka yi ma wasu Sojojin Najeriya kisan gilla ba daga Boko Haram ya fito ba, IPOB ne suka harhada bidiyon.

KU KARANTA: Gwamnatin Jigawa za ta kashe naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’

Rahoton kamfanin NAN ta ce Sagir yana mayar da martani ne game da wani bidiyo da aka yi ikirarin mayakan Boko Haram ne a cikinsa suke kashe wasu Sojojin Najeriya guda uku, wadanda suka tsugunar dasu, suka sanyasu amsa laifukansu, sa’annan suka kashesu.

Sagir yace ba’a Najeriya wannan lamarin ya auku ba, don haka ya yi kira ga jama’a da ma dakarun Sojin Najeriya, musamman wadanda suke yankin Arewa maso gabas dasu yi watsi da shi, domin ba gaskiya bane, kuma an yi shi ne don kawu rabuwar kai tsakanin yan Najeriya.

“Kiran da wani mai suna Simon Ekpa ya yi ga Sojojin Najeriya yan asalin kabilar Ibo dake aiki a yankin Arewa maso gabas dasu tsere daga rundunar su koma yankin Biyafara ne ya tabbatar da rashin gaskiyar bidiyon.

“Haka zalika kiran da yayi ga jama’an Ibo da kada su shiga aikin Soja, shi ma ya tabbatar da manufar wadanda suka shirya wannan bidiyon. Amma shugabancin rundunar Sojan kasa na jaddada manufarta na cigaba da yaki da ta’addanci. Ba zamu karaya ko mu yarda wani ya dauke mana hankali daga abin da muka sanya a gaba ba.” Inji shi.

Rundunar Sojan sama ta Najeriya ta fara samun nasara a karkashin sabon salon yaki da ta kirkiro da shi mai taken “Rattle Snake”, wanda ta ce ta kirkiro shi ne da nufin cigaba ragargaza tare da karya lagon kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel