Jega: Rashin gaskiya a Najeriya ya na karuwa fiye da sauran kasashen Afrika

Jega: Rashin gaskiya a Najeriya ya na karuwa fiye da sauran kasashen Afrika

Tsohon shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, ya shawarci kasashen Afrika su canza salon yakin da su ke yi da rashin gaskiya a halin yanzu.

Farfesa Attahiru Jega wanda ya rike hukumar INEC mai zaman kan-ta a Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2015 ya yi wannan kira ne lokacin da ya ke yin tanbihi a kan wani sabon littafi da aka buga.

A farkon makon nan ne hukumar EFCC ta kaddamar da wani littafi mai suna “Curbing Electoral Spending” (magance kashe-kashen kudi a lokacin zabe), wanda ake kira Farfesan ya yi jawabi.

An shirya wannan kaddamar da littafi ne a ranar bikin yaki da rashin gaskiya ta Duniya na bana wanda ya fado a 9 ga Watan Disamban 2019. Farfesan ya nuna cewa akwai matsala a Najeriya.

KU KARANTA: Kudin Barayi N600m, $700m sun shiga hannun EFCC a 2019

Jega ya ce: “A nan Najeriya, inda rashin gaskiya ya ke karuwa idan aka kamanta da sauran kasashen Afrika, ya kamata mu dauki wannan yaki da gaske.”

“Rana ce da za mu zauna mu yi karatun ta-natsu, mu duba tafiyar da ake ciki, mu kuma canza salo domin gano wasu dabarun yaki da rashin gaskiya.” Inji Farfesan.

Jega ya yabawa kokarin da EFCC ta ke yi wajen yakar satar dukiyar gwamnati da rashin gaskiya. Amma ya kara da cewa: “Yayin da mu ke jinjina masu, akwai bukatar su kara tashi tsaye.”

“Domin kuwa mu na ganin cewa gwargwadon kaimin da aka yi, gwargwadon yadda yakin ya ke kara wahala. EFCC su cigaba da nuna cewa babu saniyar ware wajen aikin da su ke yi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel