Ku fada mana fanshon Gwamnoni tun daga 1999 har yau – SERAP ga Jihohi

Ku fada mana fanshon Gwamnoni tun daga 1999 har yau – SERAP ga Jihohi

Kungiyar SERAP mai kokarin bin diddiki da halin tattalin arziki a Najeriya, ta rubuta takarda zuwa ga gwamnoni 36, ta na neman a fada mata fanshon da ake biyan tsofaffin gwamnoni.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust a Ranar 10 ga Disamba, kungiyar ta dogara ne da dokar FOI wanda ya ba jama’a damar samun duk wani bayani daga hannun gwamnati a kasar.

Bayan adadin fanshon da ake ba gwamnonin da aka yi a baya, wannan kungiya mai kare hakkokin ‘Yan Najeriya ta na so a ba ta kundin dokokin fanshon da kaf jihohin su ke aiki da su.

Har ila yau, wannan kungiya ta yi kira ga gwamnonin tare da shugaban kungiyar gwamnoni, Kayode Fayemi, da mataimakinsa, Aminu Tambuwal, ta fada mata ko su na aiki da wannan doka.

KU KARANTA: Kungiya ta hurowa Gwamnan Legas wuta a kan taba 'Yan Arewa

SERAP ta bukaci shugabannin NGF su kawo sunan duk wani tsohon gwamna da Jami’insa, da abin da ya ke karba lokaci bayan lokaci, sannan kuma a soke dokar da ta ba su wannan dama.

Mataimakin Darektan wannan kungiya, Kolawole Oluwadare, shi ne ya aikawa gwamnonin wannan wasika a Ranar 9 ga Watan Disamban 2019, ya na mai kira a daina biyan wannan kudi.

A dokokin fanshon, wasu tsofaffin gwamnoni kan tashi da makudan kudi da motoci da sauran abubuwan more rayuwa daga dukiyar gwamnati. A cewar SERAP, hakan sam bai dace ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel