Sa'i ya yi: Fasinja ya fadi ya mutu a filin jirgin

Sa'i ya yi: Fasinja ya fadi ya mutu a filin jirgin

- Wani fasinja da aka gano sunansa da Chukwuma Anthony Ezeh, ya fadi ya mutu a filin jirgi a Legas

- Fasinjan mai shekaru 47 kamar yadda fasfotinsa ya nuna, ya dawo ne daga kasar China

- Yana tafiya a wajen isowar matafiya ne a hanyarsa ta zuwa daukar kayansa ya fadi ya mutu

Wani fasinja da aka gano sunansa da Chukwuma Anthony Ezeh, ya fadi inda ya mutu a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Laraba.

Wani ma'aikacin filin tashi da saukar jiragen saman na Murtala Muhammad din, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya yadda fasinjan da ya iso daga kasar China ya fadi ya mutu, a yayin da yake jiran kayanshi a filin jirgin.

DUBA WANNAN: Kano: Masu nada sarakuna sun maka Ganduje a kotu

Kamar yadda bayani daga fasfotin Ezeh ya nuna, yana da shekaru 47 a yayin da wa'adinsa ya cika.

Kakakin rundunar 'yan sandan filin jirgin, DSP Joseph Alabi, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai aukuwar lamarin. Ya sanar da su ne wajen karfe 9:25 na dare a ranar Laraba. Ya ce, fasinjan ya sauka ne daga jirgin kamfanin jiragen sama na Ethiopia.

Kamar yadda yace, lamarin ya auku ne da karfe 3:15 kuma an garzaya dashi asibitin da ke filin jirgin.

"A yayin da yake tafiya a wajen isowar matafiya, ya fadi ya mutu," in ji shi.

Alabi ya kara da cewa, an adana gawar Ezeh a ma'adanar gawawwaki ta sojojin sama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel