Akwai yiwuwar za'a fara biyan marasa aikin yi albashi a Najeriya - Sanatoci

Akwai yiwuwar za'a fara biyan marasa aikin yi albashi a Najeriya - Sanatoci

- Majalisar dattawan Najeriya ta nemi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta fara wani tsari da zai dinga taimakawa marasa aikin yi

- Majalisar ta ce ya kamata gwamnati ta bude asusu da zai dinga tallafawa masara aikin yi har ya zuwa lokacin da za su samu aiki

- Haka kuma Sanatocin sun bukaci gwamnati ta kyale kamfanoni na 'yan kasuwa su dinga harkokinsu ba tare da takura ba, don hakan ne zai ba su damar daukar matasa aiki

Majalisar tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnatin shugaba Buhari da ta dauki matakai na gaggawa kan matsala ta rashin aikin yi ga al'ummar kasar.

A wata tattaunawa da suka yi jiya Laraba, bayan Ike Ekweremadu ya gabatar da wani kudiri game da matsalar rashin aikin yin, Sanatocin sun bayyana cewa rashin aikin yi ga 'yan Najeriya ba karamin kalubale bane ga kasar.

'Yan majalisar sun bukaci gwamnatin kasar da ta tanadi asusu wanda za ta dinga taimakawa marasa aikin yi har ya zuwa lokacin da za su samu aiki.

Sanatoci sun bayyana cewa yawancin matasan da suke kammala karatu a Najeriya suna nan a zaune babu aikin yi, kuma ba su samun ko kwabo na kashewa.

KU KARANTA: Dole a dinga tilasta maza suna auren mata biyu ko zinace-zinace zai ragu - In ji wata mawakiya

Majalisar dattawan ta nemi dukkanin matakan gwamnati na Najeriya da su sanya dokar ta baci akan rashin aikin yi, musamman ga matsa.

Haka kuma majalisar ta bukaci a bude wani tsari da zai dinga samar da ayyukan yi ga matasa a karkashin ma'aikatar tsare-tsare ta Najeriya.

Bayan wannan kuma majalisar ta nemi gwamnati ta bai wa manyan kamfanoni na 'yan kasuwa damar gabatar da ayyukansu ba tare da an takura musu ba, domin ta hakan ne za su iya daukar matsa suyi musu aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel