Albishir: Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta janye yajin aikin da ta fara

Albishir: Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta janye yajin aikin da ta fara

- Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa, ta janye yajin aikin da ta fara a ranar Laraba

- Shugaban kungiyar, Kwamared Joe Ajaero ya sanarwa da cewa sun janye yajin aikin da suka fara

- Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta duba bukatunsu kuma jira kawai suke a tabbatar

Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) ta janye yajin aikin da ta fara a ranar Laraba don jawo hankalin gwamnatin tarayya a kan kangin da ma'aikatanta ke ciki.

Bayan dogon taron da akayi tsakanin shuwagabannin NUEE din da gwamnatin tarayya, kungiyar ta yanke hukuncin amincewa da janye yajin aikin da ya dau tsawon kwana daya.

Kamar yadda shugaban kungiyar, Kwamared Joe Ajaero ya sanarwa jaridar Thisday, ya ce anyi nasarar shawo kan matsalolinsu a taron da aka yi.

DUBA WANNAN: Za a nada mata 5 matsayin kwamishinonin 'yan sanda - IG

Ya ce, an duba duk damuwar kungiyar da mambobinta a tattaunawar da suka yi, wacce ta kai har sa'o'in farko na yau Alhamis.

"Mun kammala tattaunawa kuma an shawo kan matsalolinmu, jira muke a tabbatar. A halin yanzu, mun janye yajin aiki," Ajaero yace.

Bayan wa'adin kwanaki 21 da NUEE ta ba ministan wutar lantarki, Saleh Mamman na tabbatar da bukatunsu tare da rashin cika sharuddan a daren Talata, yasa sun fada yajin aiki a duk fadin kasar nan a safiyar Laraba.

Yajin aikin ya kawo garkame ofisoshin kamfanonin rarrabe wutar lantarki a duk fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel