Gwamnatin Kano zata yi doakar hana aurar da 'yammata kafin su kammala sakandire

Gwamnatin Kano zata yi doakar hana aurar da 'yammata kafin su kammala sakandire

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shiri domin gabatar da sabuwar doka da zata tilasta 'yammata su kammala karatun makarantar sakandire kafin a aurar da su domin rage yawan adadin matasan jihar da basa zuwa makaranta da kuma kawo karshen aurar da yara mata masu karancin shekaru.

Sunan Najeriya ne na farko a cikin jerin sahun kasashen duniya da ke da yawan yaran da basa zuwa makaranta. Alkaluma sun nuna cewa akwai yara miliyan 13 a Najeriya da basa zuwa makaranta.

A cikin gida Najeriya, jihar Kano ce a sahun gaba da yawan yara miliyan daya da basa zuwa makaranta. Rahotanni sun nuna cewa iyayen yara a Kano sun fi aurar da 'ya'yansu mata tun suna da karancin shekaru yayin da yara maza ake tura su almajiranci, inda daga nan mafi yawansu ke kangare wa.

Domin shawo kan wannan kalubale da jihar ke fuskanta ne, gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana shirin kirkirar dokar da zata hana aurar da 'yammata kafin su kammala karatun sakandire.

Gwamnatin Kano zata yi doakar hana aurar da 'yammata kafin su kammala sakandire

Ganduje
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyaa hakan ne yayin wani taron karrama shugabanni na shekarar 2019 da hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa (NHRC).

DUBA WANNAN: Majalisar sarakuna: Gwamnatin Kano ta yi martani a kan hukucin kotu

"Maganar almajiri da ake yawan yi ta kusa zama tarihi domin yanzu mun shigar da su cikin tsarin ilimin zamani.

"Duk mun san matsalolin dake tattare da aurar da mata masu kananan shekaru, hakan ne yasa zamu yi doka da daga yanzu zata hana aurar yara mata kafin su kammala karatun sakandire," a cewar gwamna Ganduje, wanda yana daya daga cikin shugabannin da aka bawa kyautar yabo yayin taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel