Kotu ta kwace rawanin wani babban basarake, ta bukaci a maye gurbinsa da gaggawa

Kotu ta kwace rawanin wani babban basarake, ta bukaci a maye gurbinsa da gaggawa

A ranar Laraba ne babbar kotun jihar Osun ta kwace rawanin Chief Idowu Adediwura kuma ta umarci Ooni na Ife, Sarki Adeyeye Ogunwusi da ya maye gurbinsa da wani a cikin kwanaki 21.

Obalufe shi ne wazirin Ife kuma daga Ooni a mukami a masarautar sai shi.

Jastis Foluke Awolalu ta babbar kotun jihar Osun din da ke Osogbo, a hukuncinta tace an nada Adediwura ne ba tare da an bi tanadin dokokin nadin sarautar masarautar Ife din ba na 1957.

Abayomi Elugbuji ne ya shigar da karar a madadinsa da gidan sarautar Aga.

Da farko dai kotun ta yi watsi da sukar farko ta Adediwura da ta bukaci kotun ta yi watsi da karar, saboda an shigar da kara makamanciyar hakan.

DUBA WANNAN: Kano: Masu nada sarakuna sun maka Ganduje a kotu

Kotun ta kara da hana Adediwura daga bayyana kanshi a matsayin Obalufe.

A tsokacin lauyan mai kara a kan hukuncin, Babafemi Akande, ya kwatanta hukuncin da nagartacce kuma bayyananne. Ya kara da cewa, matukar aka yi nadin sarauta to ya tabbata a doka.

"Wannan dokar a bayyane take, babu wanda yafi karfin shari'a. Alkalin ya yanke hukunci ne kamar yadda doka ta tanada," Akande ya ce.

Anyi kokarin jin ta bakin Adediwura a kan hukuncin, amma abun ya ci tura. Don kuwa duk kiran wayar da aka yi mishi da sakon kar ta kwana da aka tura mishi bai amsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel