Za a nada mata 5 matsayin kwamishinonin 'yan sanda - IG

Za a nada mata 5 matsayin kwamishinonin 'yan sanda - IG

Sifeta Janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce za a kara nada wasu mata a babban matsayi a hukumar ‘yan sandan Najeriya.

Ya bayyana cewa, za a nada mata biyar a matsayin kwamishinonin ‘yan sanda a hukumar, nan ba da dadewa ba. Za a yi hakan ne don tabbatar da samun mata a babban matsayin shugabanci na hukumar.

A yayin jawabi a taron ‘yan sanda mata na shekarar 2019 a ranar Laraba, Sifeta Janar din ya ce, ‘yan sanda mata sun nuna bajintarsu tare da hazaka kuma sun tabbatar da cewa zasu iya gogayya da maza a irin wadannan wuraren masu matukar muhimmanci.

Adamu ya jaddada cewa, hukumar ‘yan sandan ta saka tsarikan jinsin. Gani da cewa za a kirkiro da ofishin mai bada shawarar da ta shafi mata da kuma ofishin bincike na mata.

Ya ce, “Mun samar da jami’ai mata wadanda ke rike da matsayi masu matukar amfani kamarsu kwamishinan ‘yan sanda, mataimakiyar sifeta janar da sauransu. Nan ba da dadewa ba zamu nada mata a mukaman shugabanci, kuma zamu nada biyar a matsayin kwamishinonin ‘yan sanda.”

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya janye takararsa ta Sanata da kotu ta ce a sake zabe

Ya bukaci taron da ya kirkiro tsare-tsaren da zasu taimakawa mata wajen shugabanci a hukumar ‘yan sandan.

Aishatu Abubakar, kwamishinan hukumar a bangarenkula da dabbobi, tace za a ba matan damar tattaunawa a kan ladabtarwa, rashawa, tsare-tsaren murabus, nauyin da ya rataya a kan ‘yan sanda mata da sauransu.

Ta bukaci da a kara nada mata a matsayin shuwagabanni don zasu iya daukar nauyin da aka dora musu.

“Muna so mu tabbatar wa da Sifeta janar cewa, zamu iya daukar duk nauyin da aka dora mana. Muna shaida mishi cewa, wannan taron zai inganta kokarin ‘yan sanda mata tare da habaka hukumar, “ Abubakar ta tabbatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel