Korafe-korafe 7 da Aisha Buhari tayi kan Garba Shehu

Korafe-korafe 7 da Aisha Buhari tayi kan Garba Shehu

A ranar Laraba, 11 ga watan Disamba 2019, uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ya saki bama-bamai kalamai kan mai magana da yawun mijinta, Malam Garba Shehu.

A jawabin da ta saki, ta yi gargadi ga Garba Shehu inda tace ba zata sake lamuntan rainin wayon da yake yi mata ba.

Legit.ng ta tattaro muku a takaicen takaitawa, korafe-korafe bakwai da Aisha ke yiwa hadimin mijinta, Malam Garba Shehu.

1. Ya ajiye aikinsa ya koma shiga sharo ba shanu

2. Ya daina biyayya ga shugaba Buhari saboda ya mayar da hankalinsa wajen biyayya ga wasu yan tsiraru da ba su al'ummar Najeriya suka zaba ba

3. Ya yi shisshigi cikin lamarin ofishinta

4. Ta tuhumceshi da Sallamar hadimanta bisa ga umurnin Mamman Daura

5. Ya ce gwamnatin Buhari ta soke ofishin uwargidan shugaban kasa

6.Ya dauki nauyin wasu yan jarida wajen rubuce-rubucen batanci gareta da yaranta

7. Garba Shehu na cikin wadanda suka shirya cin mutuncinta ta hanyar sakin bidiyon da diyar Mamman Daura, Fatima, tayi na nuna cewa na hana Aisha shiga fadar shugaban kasa kuma ya san ba gaskiya bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel