Daga yau, yan Afrika zasu iya shigowa Najeriya kyauta, ba bukatan biza - Buhari ya yi shela

Daga yau, yan Afrika zasu iya shigowa Najeriya kyauta, ba bukatan biza - Buhari ya yi shela

Daga kasar Masar, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shelar cewa duk wani dan nahiyar Afrikan da ke bukatar shigowa Najeriya zai iya shigowa ba tare da biza ba.

Buhari ya bayyana hakan ne a taron zaman lafiya da cigaban nahiyar Afrika dake gudana a birnin Aswan, kasar Masar.

Ministan harkokin wajen kasar Somaliya, Ambasada Ahmed Awad ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Tuwita da yammacin Laraba, 11 ga watan Disamba, 2019.

Ambasada Awad yace: "Ina mai matukar yabawa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da yayi sanarwa a taron Aswan cewa an togaciyewa dukkan yan Afrika bizan shiga Najeriya.

Daga Junairun 2020, yan Afrika zasu rika shiga Najeriya ba tare da biza ba. Wannan abun koyi ne mai kyau, mun gode ranka shi dade."

DUBA NAN: Bayan makonni biyu da bashi beli, Kotu ta bada umurnin ajiye 'dan Maina a gidan Yari

A taron, Shugaba Muhammadu Buhari ya siffanta yin sulhu tsakanin kasashen hamayya a nahiyar Afrika shine babban hanyar kawo cigaba nahiyar gaba daya.

Yayinda yake jawabi ranar Laraba a zaman bude taron zaman lafiya da cigaban nahiyar Afrika dake gudana a birnin Aswan, kasar Masar, shugaba Buhari yace: "A matsayinmu da yan Afrika, yana da muhimmanci mu mayar da hankali kan dakile rikici da sulhu."

"Rikice-rikice na da hadari matuka ga al'ummarmu kuma yana kawo cikas wajen cigabanmu. Saboda haka, ba zamu gushe muna da'awar daina rikici ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel