Yanzu-yanzu: Bayan makonni biyu da bashi beli, Kotu ta bada umurnin ajiye 'dan Maina a gidan Yari

Yanzu-yanzu: Bayan makonni biyu da bashi beli, Kotu ta bada umurnin ajiye 'dan Maina a gidan Yari

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birni tarayya Abuja ta bada umurnin mayar da dan gidan mutumin da ake zargin da handamar kudaden yan fansho,Abdulrashid Maina, wato Faisal Maina, a gidan gyara halin garin Kuje, Abuja.

Faisal Maina yana gurfana a kotu ne kan zargin rashawa kumaya kasance hannun jami'an yan sanda.

Amma a yau Laraba, Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya baya umurnin mayar da shi kurkuku bisa ga bukatar lauyan Faisal, Mohammed Munguno, wanda ya bukaci kotun ta mayar da shi gidan gyara halin Kuje.

An gurfanar da Faisal ne ranar 25 ga watan Oktoba kan zargin aikata laifuka uku na safarar kudade, da zamba.

A ranar 26 ga Nuwamba, Alkali mai shari'a, Jastis Okon Abang, ya baiwa Faisal beli kan farashin milyan sittin da kuma mai tsaya masa.

Jastis Abanga ya bayyana cewa wajibi ne wanda zai tsaya masa ya kasance dan majalisan wakilan tarayya kuma ya kasance ya mallaki dukiya a Abuja.

Ya ce wajibi ne wanda zai tsaya masa ya rako Faisal kotu duk ranar da kotu ke bukatanshi har zuwa karshen karar.

Ya kara da cewa duk lokacin da wanda ya tsaya masa yaki zuwa kotu, za'a janye belin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel