Kuskure mafi girma da Buhari zai yi a rayuwarsa - Fani Kayode

Kuskure mafi girma da Buhari zai yi a rayuwarsa - Fani Kayode

Jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode yace babban kuren da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai yi shine bada hanci ko tursasa kotun koli ta soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Wannan maganar ta fito ne bayan da sashin jam'iyyar PDP na Kudu maso Yamma suka zargi shirye-shiryen Shugaban kasar na kwace nasarar Gwamna Makinde a kotun koli.

Ya sanar da hakan ne a wani taro da jiga-jigan jam'iyyar PDP suka hallara. Sun hada da Yemi Akinwonmi, Sanata Ibrahim Kazaure, Dr. Eddy Olafeso, Dr. Doyin Okupe da sauransu.

Jam'iyyar PDP ta ce, "muna son kara jaddadawa a fili cewa, jam'iyyar PDP ta yi nasara a kan APC a zaben gwamnoni na jihar Oyo. Ta yi nasara a kananan hukumomi 28 inda APC ta samu 5 kacal."

DUBA WANNAN: Kano: Masu nada sarakuna sun maka Ganduje a kotu

"Hukuncin da zai yi wa jama'ar jihar dadi kuwa shine tabbatar da nasara ga PDP a zaben. Adedibu da APC ba zasu iya kwace wannan nasarar ba, duk kuwa kotun da za a je. Hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ce za ta tabbata," ya kara da cewa.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na tuwita a ranar Laraba, tsohon ministan ya shawarci Shugaban kasa da kada ya yi kuskuren bin wannan hanyar, saboda hatsarin da za ta iya kawowa.

"Babban kuskuren da Muhammadu Buhari zai yi shine bada cin hanci ko tirsasa kotun koli wajen soke zaben Seyi Makinde a matsayin Gwamnan jihar Oyo. Ina bashi shawarar cewa, wannan hanyar na da babban hatsari mai yawan gaske," ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel