Damfara: Amurka ta kwace jirgin saman wani attajirin dan Najeriya

Damfara: Amurka ta kwace jirgin saman wani attajirin dan Najeriya

Mahukunta a kasar Amurka sun kwace jirgin sama mallakar wani dan Najeriya da ake tuhuma da aikata damfara ta miliyoyin daloli a kasar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An kwace jirgin ne a ranar Talata a filin tashi da saukan jirage na Peachtree DeKalb a jihar Georgia kamar yadda WSB-TV ta ruwaito.

An ruwaito cewa jami'an tsaro na FBI suna caje jirgin domin neman hujojji a kansa yayin da wasu tawagar jami'an tsaron suka bazama neman miyagun kwayoyi da sauran haramtattun ababe.

Sai dai kawo yanzu mahukunta kasar ta Amurka ba su bayyan sunan dan Najeriyan da ya mallaki jirgin saman ba.

Daya daga cikin jami'an na FBI ya ce," Galibu mutane ba su fahimta, ba su san abinda ke faruwa a Atlanta, Georgia ba."

DUBA WANNAN: Cike da alfahari: Hotunan Buhari da Hanan bayan ta kammala digiri da sakamako mafi daraja

"Wannan aikin da muke yi kullum kenan, wannan shine nasarar da muka samu sakamakon hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro na jihohi da tarayya domin mu damke miyagu a wurin abin zai musu zafi.

"Da zarar mun ga wani irin samfurin jirgin sama, muna zargin ana aikata ba dai-dai ba."

A watan Nuwamba ne jami'an tsaro a Amurka suka samu shugaban Air Peace, Allen Onyema da laifin karkatar da $20 miliyan daga Najeriya zuwa wasu asusun bankuna na Amurka ta hanyar amfani da takardun bogi.

An ce Onyema yana yawaita tafiye-tafiye zuwa Atlanta inda ya bude asusun bankuna da yawa. Tsakanin 2010 zuwa 2018 an ce an tura masa $44.9 miliyan daga wasu asusun bankuna na kasashen waje.

Wata kotun Amurka a arewacin Georgia ta bayar da umunrin kamo Onyema inda ta bawa jami'an tsaro na kasar su damko shi.

Sai dai, attajirin dan kasuwan ya musanta aikata duk laifin da aka ce an same shi da aikatawa kuma ya sha alwashin wanke kansa daga zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel