An kwashi 'yan kallo a kotu yayin da 'yar uwar Maina ta bayar da shaida a kansa

An kwashi 'yan kallo a kotu yayin da 'yar uwar Maina ta bayar da shaida a kansa

An yi karamin wasan kwaikwayo a babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Laraba. Fatima Abdullahi, kanwar Abdulrasheed Maina ta bayyana gaban kotun don bada shaida a kan tsohon Shugaban hukumar fansho ta kasa.

Fatima ma’aikaciyar gwamnati ce kuma tana zaune a Kaduna, ta sanar da kotun cewa iyayensu daya da Maina.

Ta bada shaidar ne a yayin da take gefen kotun ta inda alkalin kadai ke iya ganinta. Jastis Abang, a yayin zaman kotun yana iya jin muryar Fatima ne ta hanyar amfani da amsa kuwwar kotun da ta yi.

Amma kuma, a yayin da take bada shaida, daya daga cikin lauyoyi Common Input & investment Limited ya zargi cewa tana karanto shaidar ne daga takardar da aka shirya mata.

A yayin da aka tambaya wacce ake karar ko karanta shaidar take, ta ce zasu iya zuwa su duba ta, domin kuwa jakar hannunta ce kadai a tare da ita. “Dalilin da yasa nake yi a hankali shine don in ba alkalin damar daukar shiftar abinda nake fadi.” In ji Fatima.

Alkalin ya bayyana cewa, bai ga wacce take bada shaidar da kowacce takarda ba.

DUBA WANNAN: Wani bakatsine ya sauya sunansa daga Buhari zuwa Sulaiman

Kamar yadda Fatima Abdullahi ta sanar, bata da masaniyar komai a kan kamfanin da ake magana. “A watan Augusta na 2019, naje cire kudi amma sai hakan ya gagara. Kawai sai na shige bankin don mika koke na ga manajan. Bayan zaman jira na sa’a daya da nayi, ya sanar dani cewa in kara jira don jami’an EFCC zasu iso. Sun iso suka tafi dani ofishinsu inda suka fara tuhumata a kan kamfanin. Amma sai na sanar musu bani da masaniya a kai,”

“Na rubuta abinda na sani kuma sun bukaci da in kai kaina ofishinsu na Abuja. Washegari na isa ofishinsu na Abuja tare da lauyana. Sun kara tambaya ta kan kamfanin tare da nuna mini takardar rijistarshi mai kunshe da Fatima Samaila Abdullahi da ranar haihuwata. Na sanar dasu ban sani ba. Hasalima, ni ina amfani ne da Fatima Abdullahi kuma lambar wayar da ke jiki ba tawa bace.

“An rufe min duk asusun bankuna na. Hatta wanda nake albashi dashi an rufe min. Bansan komai a kai ba.”

Mai bada shaidar tace, bata da masaniya a siyan hannayen jari a kamfanin. Ta kara da cewa hoton da ke dauke a kan takardun tsohon hotonta ne, tun tana karama kafin ta yi aure.

A halin yanzu, an dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel