Zan yunkuro a 2023 - Shehu Sani ya kalubalanci El-Rufa'i

Zan yunkuro a 2023 - Shehu Sani ya kalubalanci El-Rufa'i

Tsohon Sanatan da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisa ta 8, Shehu Sani ya bayyana cewa zai fito takara a zaben 2023 mai zuwa. Ya kara da bayyana cewa, babu abinda zai tsorata shi.

Idan zamu tuna, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce yayi wa Sanata Shehu Sani da Sanata Sulaiman Hunkuyi murabus a siyasa. Ya kara da lissafa wasu 'yan siyasa wadanda suka sha mugun kaye a wancan zaben da ya gabata.

Amma kuma, a jawabin da Sanata Sani ya yi a ranar Laraba, jim kadan bayan ya karba lambar yabo daga zauren dattijan Sabon Garin Nassarawa a Kaduna, ya ce: "Bamu hakura da siyasar Kaduna ba, kuma zamu dawo.

"Babu tsoron komai a ranmu kuma babu abinda zai firgitamu ko ya hanamu fitowa takara a 2023. Lokacin da mutanenmu suka so mu dawo, zamu dawo," Sani ya jaddada.

DUBA WANNAN: Wani bakatsine ya sauya sunansa daga Buhari zuwa Sulaiman

Sani, wanda mai rajin kare hakkin dan Adam ne, ya yi bayanin cewa, a lokacin da yake kujerar Sanata a majalisar kashi na 8, ya dage wajen kare nagarta da kuma cin gashin kan majalisar.

Kamar yadda yace, majalisar tarayyar karo ta 8 din ta tsaya tsayin daka wajen kare damokaradiyya. Ta kara da duba rinjaye da karfin ikon da ake ba zababbu ta hangar duban abinda kundin tsarin mulki ya tanadar ba tare da tsoro ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel