Jiragen yakin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram luguden wuta, sun konasu kurmus

Jiragen yakin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram luguden wuta, sun konasu kurmus

Rundunar Sojan sama ta Najeriya ta fara samun nasara a karkashin sabon salon yaki da ta kirkiro da shi mai taken “Rattle Snake”, wanda ta ce ta kirkiro shi ne da nufin cigaba ragargaza tare da karya lagon kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Daraktan watsa labaru na rundunar sojan sama, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, inda yace tuni sabon salon yakin ya fara samar da sakamakon da ake bukata.

KU KARANTA; Sanatoci sun yi tutsu ga takwarorinsu dake kokarin tsige shugaban majalisar dattawa

“A ranar farko da muka kaddamar da salon, jiragen yakinmu sun yi ma mayakan Boko Haram ruwan wuta ta yadda da dama daga cikinsu suka kone kurmus tare da lalata sansanoninsu da babban sansanin tsare hare harensu dake Parisu, da Garin Maloma, dukkaninsu a cikin dajin Sambisa.” Inji shi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kafin rundunar ta kaddamar da wadannan hare hare sai da ta gudanar da cikakken bincike, baya ga tattara sahihan bayanai dake tabbatar da taruwar yan Boko Haram a sansanonin.

“A sansanin Parisu, mun gano akalla yan ta’adda guda 30 ta hanyar amfani da jirgin leken asiri, da wannan ne muka aika jirgin yakinmu wanda ya sauke musu ruwan wuta a daidai inda suke, kuma ya tafka musu barna.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Gombe ta yi nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, matashi dan shekara 20, Yusu Umar tare da abokin ta’asarsa, Nasiru Hassan dan shekara 28.

Kaakakin Yansandan jahar, SP Mary Malum ce ta tabbatar da kama miyagun mutanen a ranar Talata, 10 ga watan Disamba yayin da take gabatar dasu ga manema labaru a babban ofishin rundunar Yansandan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel