Kudin fansho: Yadda EFCC ta gano asusun banki da dumbin kadarori da sunan dan Abdulrashid Maina

Kudin fansho: Yadda EFCC ta gano asusun banki da dumbin kadarori da sunan dan Abdulrashid Maina

A ranar Laraba ne wani jami'in hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ya bayyana yadda suka gano asusun banki da dumbin kadarori da sunan Faisal, dan Abdulrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran harkar fansho.

Jami'in na EFCC mai suna Mohammed Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da shaida a gaban wata kotun Abuja a cigaba da sauraron karar Faisal.

A cewar jami'in, a shekarar 2010 ne aka kafa wata tawagar jami'an EFCC domin gudanar da bincike a kan asusun 'yan fansho a ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya da rundunar 'yan sanda.

"Maina ya kasance a cikin jerin mutanen da zamu gudanar da bincike a kansu saboda kasancewarsa shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin sake fasalin harkokin da suka shafi fansho. A yayin da muke gudanar da bincike a kansa ne muka ci karo da sunan Faisal," cewar jami'in.

Sannan ya cigaba da cewa, "bincikenmu ya gano yadda Maina ya karkatar da kudaden 'yan fansho zuwa wasu asusun kamfanoni da sunan kwangila. Mun bi diddigin takardun kamfanonin har zuwa ofishin hukumar rijistar masana'antu (CAC), sannan mun bi sunayen masu kamfanin da darektocinsu domin sanin su waye su."

Goje ya kara da cewa sun ci karo da sunan Faisal a cikin takardun da suka samu daga asusun ajiyar kamfanonin da kuma wasu kadarori masu dumbin yawa.

Kazalika, ya bayyana EFCC sun nemi Faisal ya bayyana kadarorinsa bayan an kama shi tare da mahaifinsa a cikin watan Satumba, 2019.

A cewar jami'in, sun gano asusun banki dauke da makudan kudi da wani katafaren gidan gona da gidaje a Kaduna, Borno da Abuja da sunan Alhaji Faisal A. Abdullahi.

"Mun gano cewar ba wani ne Alhaji Faisal A. Abdullahi ba face Faisal, dan gidan Albdulrasheed Maina, kuma shine da kansa ya rubuta sunan a jikin takardar bayyana kadarori da ya cike. Ya fada mama cewa Abdullahi sunan kakansa ne," a cewar Goje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel