An kori dan kwallon Najeriya daga kulob din da yake a Turai bayan ya dirkawa 'yar gidan shugaban kungiyar cikin shege

An kori dan kwallon Najeriya daga kulob din da yake a Turai bayan ya dirkawa 'yar gidan shugaban kungiyar cikin shege

- An gano cewa, wani matashin dan kwallon kafa daga Najeriya an koreshi daga kungiyar da yake bugawa wasa a turai

- Hakan ta faru ne, bayan da ya dirkawa budurwarshi kuma 'yar shugaban kungiyar ciki

- Ya ce, abun ya bashi mamaki don kuwa shi da masoyiyar tashi duk sun mallaki hankalin kansu

Wani rahoto da jaridar ghanaScoocer.net ta ruwaito, ta bayyana cewa wani matashin dan kwallon Najeriya da aka boye sunanshi an koreshi daga kungiyar kwallon kafa ta kasar Slovenia. An yi hakan ne bayan da ya dirkawa 'yar shugaban kungiyar ciki.

Rahoton ya bayyana cewa, tuni dan kwallon kafar ya dawo Najeriya.

Da dan kwallon kafar ke bayyana abinda ya faru, ya ce budurwarshi wadda 'yar shugaban kungiyar da yake ce, ta sanar dashi cewa tana da ciki, labarin da ya kai kunnen mahaifinta.

Daga nan an bukaci jin ta bakinshi inda ya tabbatar da cewa ciki nashi ne. Ya ce, wakilinshi ne daga baya ya sanar da shi cewa an koreshi.

KU KARANTA: San barka: Hadiza Gabon ta taimakawa samari masu tuyar kosai da jari

Ya bayyana cewa, abun ya bashi matukar mamaki don kuwa shi da yarinyar duk sun mallaki hankalin kansu. Wakilinshi amma ya tabbatar mishi da cewa, zai garzaya FIFA don a kwatar mishi hakkinshi.

Dan kwallon ya ce, ya rattaba hannunshi a kan kwangilar tsakaninshi da kungiyar wasan na shekaru 3 da kuma damar shekara daya, kafin aukuwar wannan lamarin.

Ya ce babban abun takaicin shine yadda suka hana budurwar tashi magana dashi a kafafen sada zumuntar zamani. Hakazalika, sun hana abokan aikinshi kula shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel